Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Tarayya Na Sa Ran Samun Naira Biliyan 400 Daga Kadarorin Ta Da Za Ta Sayar A 2018

Published

on

Gwmanatin Tarayya tana sanya ran tara naira biliyan 400 wanda ta yi daidai da dala n 1.3 ta hanyar sayar da kadarorin ta da za ta yi a wannan shekarar don taimakawa wajen zuba kudi a cikin kasafin kuin ta na shekarar 2018.

A hirar sa da kafar dillancin labarai ta Reuters, Darakta Janar na hukumar sayar da hannun jari na kasa (BPE) Aled Okoh ya ce, gwamnatin ta kammala dukkan shiye-shirye don fara sayar da shirin kamfanin samar da wutar lantarki ta hanyar karbar bashin dala biliyan daya daga bankin

duniya don bunkasa rabarwar da kuma samar da wutar wadda bata tafiya kamar yadda ya kamata.

Okoh ya ci gaba da cewa, gwamnatin ta lissafa kadarori guda sha daya data tsara a wannan shekarar kodai don jingonarwa masu zuba jarin da suka dace ko kuma sayarwa da kamfanoni masu zaman kansu wadanda kuma suka hada da daga wutar lantarki da filayen wasanni.

Wata majiya ta bayyana cewar, gwamnatin na shirin sayar da wani yankin ta na kamfanin Nigerian Reinsurance ta hanyar a cikin watan Nuwamba.

A shekarar 2013, Nijeriya ta fara sayar da hannun jarin wani sashen kamfanin ta samar da wutar lantarki da ya durkushe wanda aka sanya ran zai inganta samar da wutar lantarfkin da kuma da kuma zuba biliyoyin daloli a zabon zuba jari, amma babu daya da ya auku.

A cewar Okoh, fanin na samar da wutar lantarki, yana daya daga cikin kashi talatin da bakwai bisa dari da aka sayar da hannun jarin ta wadda kuma bata gudanar da wani katabus kuma ba tare da samar da wasu alkaluma akan ko kadarori nawa aka sayar ba.

Darakta Janar ya sanar da cewar, Nijeriya ta janyo ra’ayin masu son zuba jari na dala biliyan 7.8 daga kasar waje da kuma kamfani masu zaman kansu guda hamsin da uku.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, har yanzu bai sanya hannu akan dokar tsarin kudin da za a kashe na 2018 ba.

Majalisar Kasa kuwa, ta amince da kasafin kudi na naira tiriliyan 9.12 wanda ya kansance ya haura da naira tiriliyan 8.61 da gwamnatin ta gabatarwa da ‘yan majalisar.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: