ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, November 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Tarayya Na Shirin Dakatar Da Shigo Da Kifi Daga Ketare

by Abubakar Abba and Sulaiman
4 months ago
Kifi

Gwamnatin Tarayya ta kuduri aniyar dakatar da shigo da Kifi daga kasashen ketare, wanda aka jima ana yi fitonsa.

A cewar gwamnatin tarayyar, za ta kawo karshin hakan ne ta hanyar bunkasa kamun Kifin a cikin gida Nijeriya.

  • Sin Da EU Suna Kokarin Samun Moriyar Juna A Shekaru 50 Masu Zuwa
  • An Amince Da Biranen Kasar Sin 9 A Matsayin Biranen Dausayi Na Kasa Da Kasa

Kazalika, za ta yi hakan ne, musamman domin kara karfafa samar da wadataccen abinci a kasar da samar da ayyukan yi da kuma kara karfafa fitar da kayan da ba su shafi fannin mai ba.

ADVERTISEMENT

Ministan Bunkasa Tattalin Arzikin Teku, Adegboyega Oyetola ne ya sanar da hakan, a yayin wata ganawa da shugabanin kungiyoyin masu kamun Kifi a Abuja.

Ma’aikatar Ministan ce ta shirya ganawar, kan kokarin da gwamnatin tarayya ke ci gaba da yi, na saita fannin kamun Kifin a kasar.

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Ya Zuba Naira Tiriliyan 1.5 Don Bunkasa Noma Da Kayan Aiki Na Zamani

Dalilin Asusun NADF Na Yin Hadaka Da Gwamnatin Jihar Jigawa

“Dole ne kasar nan ta samar da wata sabuwar hanya, domin samar da Kifin da zai wadace ta, wanda hakan zai kuma taimaka matuka wajen rage dogaro da shigo da Kifin daga kasashen waje da kuma kara habaka fannin” in ji Ministan.

Oyetola ya kara da cewa, gwamnatin tarayya ta himmatu kwarai da gaske wajen bai wa fannin goyon bayan da ya dace, musamman ta hanyar yin amfani da tsarin kimiyyar fasahar zamani da kuma zuba makudan kudade a fannin.

Kazalika, ya jaddada cewa; gwamnatin tarayya za ta kara kaimi wajen ganin ana samar da wadataccen Kifi a kasar, musamman domin rage dogaro a kan wadanda ake shigowa da su daga kasashen ketare, duba da cewa; fannin na bayar da gagarumar gudunmawa wajen kara bunkasa tattalin azikin kasar.

Kungiyoyiyon da suka halarci ganawar sun hada; manya-manyan masu ruwa da tsaki a fannin na kamun Kifi, kungiyar masu kamun Kifi ta kasa (FCFN), kungiyar masu kama dabbobin ruwa (TADAN), kungiyar masu kiwon Tarwada ta kasa (CAFAN) da sauran makamantansu.

Babban mai bai wa ministan shawara a fanin yada labarai, Bolaji Akinola, a cikin sanwar da ya bayar; bayan kammala taron ya bayyana cewa; Oyetola ya shaida wa mahalartan cewa, ma’aikatar na kara yin kokari wajen tallafa wa mata da matasa da suka rungumi sana’ar yin kiwon Kifi a karkashin shirye-shiyen da ma’aikatar ta kirkiro.

A cewar ministan, wannan shiri ne na tallafa wa mata da matasa; wanda kuma ya hada da tallafa musu da rance da kayan aiki, musaman don kara musu kwarin gwiwa, domin bayar da tasu gudunmawar wajen kara bunkasa fannin a Nijeriya, wanda kuma ya yi daidai na shirin Shugaban Kasa Bola Tinubu (Renewed Hope Agenda).

“Kara yawan matasan da za su rungumi sana’ar kiwon Kifi, wani babban maki ne, na kara samar da wadataccen abinci a fadin wannan kasa, wanda hakan zai kuma kasance wani mataki ne na rage marasa yin aiki a kasar” a cewar Oyetola.

“Mun mayar da hankali wajen tabatar da cewa, ba a bar mata da matasan kasar nan a baya ba, musamman don ganin an inganta rayuwarsu”, in ji Ministan.

A wajen ganawar, masu ruwa da tsaki a fannnin; sun kuma bijiro da wasu kalubale da ke ci gaba da ci wa fannin tuwo a kwarya.

A cewarsu, kalubalen sun hada da; yawan kamun Kifayen a Kogi, rashin samun rance, karancin kayan adana Kifin da ake adana Kifin bayan kamo su.

Sauran su ne, tsadar abincin da ake ciyar da su, wadanda ake shigo wa da su daga ketare, matsalar safararsu, karbar haraji barkatai, wanda ke sanyawa matasa ba sa iya shiga cikin sana’ar.

Sai dai, Oyetola ya bai wa masu ruwa da tsakin tabbacin cewa, wadannan kalubale da suka bijro da su, ma’aikatar za ta lalubo da mafita a kansu.

A cewarsa,  a yanzu ana kan tattaunawa da Bankin Duniya, musamman domin a samu rancen kudi don tallafa wa masu kiwon Kifin a kasa tare da kuma samar musu da Inshora.

Ministan ya ci gaba da cewa, wannan zai kara tabbatar da nasarar da aka samu a shirin zamani na kamun dabbobin ruwa a Dam din Oyan da kuma sauran yankunan da ma’aikatar tasa ta yi hadaka da ma’aikatar albarkatun ruwa ta tarayya da sauran hukumomin gwamnatin tarayya.

“Wannan ganawa, ba iya nan za ta tsaya ba; amma tamkar yanzu ne aka fara ta, domin za a ci gaba da tattaunawa kan yadda za a ci gaba da habaka fannin,” in ji shi.

Shi kuwa a nasa jawabin, Wellington Omoragbon, Daraktan kula da kamun Kifi da sauran dabbobin ruwa, ya sanar da muhimmancin bukatar kara karfafa hadaka, domin jawo masu son zuba hannun jari a fannin, musamman domin a kara samar da wadataccen Kifi a fadin kasar baki-daya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tinubu Ya Zuba Naira Tiriliyan 1.5 Don Bunkasa Noma Da Kayan Aiki Na Zamani
Noma Da Kiwo

Tinubu Ya Zuba Naira Tiriliyan 1.5 Don Bunkasa Noma Da Kayan Aiki Na Zamani

November 14, 2025
Rashin Daukar Tsauraran Matakai Na Iya Durkusar Da Bangaren Noma – Shehu Galadima
Noma Da Kiwo

Dalilin Asusun NADF Na Yin Hadaka Da Gwamnatin Jihar Jigawa

November 14, 2025
Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista
Noma Da Kiwo

Shirin Shugaba Tinubu Na ‘Renewed Hope’ Zai Karfafa Wa Manoma Gwiwa – Oyebanji

November 7, 2025
Next Post
Manyan Nasarorin Da Dakta Dantsoho Ya Samar Tun Darewarsa Shugabancin NPA

Manyan Nasarorin Da Dakta Dantsoho Ya Samar Tun Darewarsa Shugabancin NPA

LABARAI MASU NASABA

An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing

An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing

November 16, 2025
Ana Mai Da Hankali Kan Dabarun Kasar Sin A Fannin Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya A Taron COP30

Ana Mai Da Hankali Kan Dabarun Kasar Sin A Fannin Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya A Taron COP30

November 16, 2025
Wata Ƙungiya Ta Fara Bin Digdigin Takardun Karatun Matawalle

Wata Ƙungiya Ta Fara Bin Digdigin Takardun Karatun Matawalle

November 16, 2025
DSS

Hukumar DSS Ta Kama Wani Kan Zargin Ƙerawa Da Rarraba Makamai A Filato

November 16, 2025
ECOWAS

A Zamanantar Da Tsarin Karatu A Makarantun Koyar Da Ilimin Addinin Musulunci – ECOWAS

November 16, 2025
APOSUN Ta Jaddada Aniyarta Na Daƙile Hada-hadar Haramtattun Kuɗaɗe

APOSUN Ta Jaddada Aniyarta Na Daƙile Hada-hadar Haramtattun Kuɗaɗe

November 16, 2025
Yadda Za A Magance Yawan Faɗace-faɗace A Wasannin Gasar Firimiyar Nijeriya

Yadda Za A Magance Yawan Faɗace-faɗace A Wasannin Gasar Firimiyar Nijeriya

November 16, 2025
Kwankwaso

NNPP Tana Da Ƙwarin Gwiwar Riƙe Kano Da Lashe Jihohin Arewa A Zaɓen 2027 – Ajuji

November 16, 2025
Meke Kawo Yanke Hukunce-hukunce Masu Karo Da Juna Daga Kotuna?

Meke Kawo Yanke Hukunce-hukunce Masu Karo Da Juna Daga Kotuna?

November 16, 2025
Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN Sun Shaida Adawar Sassan Kasa da Kasa Da Burin Masu Tsattsauran Ra’ayi Na Japan Na Ruguza Odar Kasa Da Kasa Ta Bayan Yakin Duniya Na 2 Dangane Da Batun Taiwan

Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN Sun Shaida Adawar Sassan Kasa da Kasa Da Burin Masu Tsattsauran Ra’ayi Na Japan Na Ruguza Odar Kasa Da Kasa Ta Bayan Yakin Duniya Na 2 Dangane Da Batun Taiwan

November 15, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.