A halin yanzu gwamnatin tarayya ta sanya hannu a karbar bashin dala biliyan 3.45 daga Bankin Duniya wanda ake sa ran za a yi amfani da su wajen gudanar da manyan ayyuka a bagarorin samar da wutar lantarki, bunkasa ilimin mata da sauran bangaren tattalin arziki.
Ministan Kudi da tattalin arziki, Wale Edun ya bayyana haka a tattaunawarsa da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan kammala taron majalisar zartarwa da shugaba Tinubu ya jagoranta ranar Litinin.
Ya kuma ce, bashin zai matukar taimakawa wajen aiwatar da ayyukan ci gaba musamman in aka kuma hada kudaden da za a tattara na cikin gida, musamman ganin ba za a fara biyan bashin ba sai nan da shekara 10 kuma ruwan da aka dorawa bashin bashi da wani yawa.
Ya ce, “A taron majalisar zartaswa da aka yi yau an amince da takardun karbar bashi daga Bankin Duniya da kuma wasu kungiyoyin bayar da tallafi na duniya don aiwatar da wasu manyan ayyuka. Ayyukan sun hada da samar da wutar lantarki da ilimin mata a fadin tarayyar kasar nan.
Za a samar da wasu kudaden ga jihohi don taimaka musu karfafa cibiyoyinsu na tatsar kudaden haraji a cikin gida.
“Akwai Shirin karfafa ilimin mata ta hanyar samar musu tallafin da zai taimaka musu fuskantar karatu a fadin kasar nan.
“Saboda haka basuka biyar da muka karba na Dala Biliyan 3.45 zamu biya ne a cikin shedkara 40 ruwan bashin kuma babu yawa, za mu fara biyan zangon farko nan da shekara 10 shima babu ruwa gaba daya” in ji shi.