Abubakar Abba" />

Gwamnatin Tarayya Ta Kashe Naira Tiriliyan 2.95 Wajen Shigo Da Man Fetur A 2018 –NBS

A bisa bayanan da aka samo daga gun Hukumar Kididdiga ta kasa NBS a ranar Litinin data gata sun nuna cewar, Gwamnatin Tarayya ta kashe jimlar naira tiriliyan 2.95 a shekarar 2018 wajen shigo da man fetur samfarin PMS, inda hakan ya kai kusan kashi 50 na kudin data kashe.
Adadin ya kuma nuna cewar, Nijeriya ta kashe naira tiriliyan 1.97 wajen shigo da man fetur samfarin PMS a 2017 da kashe naira tiriliyan 1.63 a 2016 da kuma kashe naira tiriliyan 1.14 a 2015.
Yawan man da aka shigo dashi ya kai kashi 22.4 na jimlar wanda aka shigo dashi a shekarar 2018, inda ya kuma haura zuwa kashi 20.6 a shekarar 2017 da zuwa kashi 18.4 a shekarar 2016 da kuma zuwa kashi 17 a shekarar 2015.
Kamfanin NNPC ne keda alhakkin shigo da man kusan sama da shekara daya ganin cewar, yan kasuwa masu shigo da man a baya, sun daina shigo dashi saboda karancin kudin musaya na kasar waje da kuma karin da akayi na farashin danyen mai, inda hakan ya janyo karin farashin sauke man ya karu sama da farashin sayar da man akan lita naira 145.
Acewar bayanan da aka samo daga Kamfanin PPMC daya daga cikin bangarorin NNPC shigo da PMS, wanda yake akan litoci miliyan 56.5 a kullum a Janairu, ya karu sama da Ipd miliyan 86.4 a Fabirairu.
Man ya kai Ipd miliyan 66.8 a Maris a cikin Afirilu ya kai Ipd miliyan 70.7 a cikin Mayu ya kai Ipd miliyan 36.7, inda kuma a Mayu da Yuni ya kai Ipd miliyan 34.5.
Har ila yau, a Yuli ya kai Ipd miliyan 36.5 a Juli ya kai Ipd miliyan 58.4 a Agusta ya kai Ipd miliyan, inda kuma a Satumba ya kai Ipd miliyan 57.8.
Fashin bakin da akayi akan adadin da aka samo daga PPMC da kuma DPR ya nuna cewar, a kalla an shigo da litocin man miliyan 55.1 a kullum a cikin watanni tara idan aka kwatanta da Ipd miliyan 48.5 a 2016.
Bayanan da aka samo daga DPR sun nan cewar, shigo da PMS ya kai Ipd miliyan 49.2 da Ipd miliyan 49.8 a 2015 da kuma a 2016.
A Okutobar 2018, Majalisar Dattawa ta fara gudanar da buncike akan haramtaccen biyan kudin tallafin rarar mai na PMS, amma NNPC ta karyata cewar, kudin tallafin na rara man dala biliyan 3.5 baya gun ta.
Har ila lau, Majalisar ta kafa karamin kwamiti don ya gudanar da bincike akan asusun da NNPC ya ajiye dalar biliyan 3.5, inda NNPC ya ce, shine ya kikiro tara kudin gidauniyar dala biliyan 1.05 gannin cewar shine kadai yake shigo da man da kuma rabar dashi a daunacin fadin kasar nan, inda Kamfanin ya kara da cewar, kudin suna ajiye a Babban Bankin Nijeriya CBN.
Manajin Darakta na Rukunonin Kamfanin PPMC Umar Ajiya, a cikin kasidar sa da ya gabatar a wani taron masana’antu a Nuwamba ya bayyana cewar, sabawa dokokin iyakokin kasashe, ya kara janyo yin fasakaurin mai, inda a kullum ake fitar da Ipd miliyan 35 wanda kuma ya kai sama da Ipd miliyan 55.
Shi kuwa Babban Manajin Darakta na Rukunonin Kamfanin NNPC Dakta Maikanti Baru a Maris din 2018 ya yi nuni da cewar, bude gidajen mai barkatai da akeyi sun kara janyo yin fasakaurin man zuwa kasashen da suke makwabtaka da Nijeriya, inda hakan yake janyo tirniki wajen wayar da kai ga wadanda suke a cikin fannin.
Acewar Babban Manajin Darakta na Rukunonin Kamfanin NNPC Dakta Maikanti Baru, hakan ya janyo cin kasuwar man na Nijeriya a kasashen Nijar, Benin, Cameroon, Chad, Togo da kuma Ghana, wadanda basu da iyakoki kai tsaye da Nijeriya.
A karshe Baru ya ce, NNPC naci gaba da nuna damuwar sa akan fasakaurin na iyakokin kasa, inda hakan ke dannewa yan Nijeriya more romon dimokaradiyyar da ya kamata su amafana bayan da Gwamnatin Tarayya ta sanya farashin mai akan naira145 na ko wacce lita daya duk da karin farashin PMS a kasuwar bayan fage zuwa naira171 na ko wacce lita daya.

Exit mobile version