Gwamnatin tarayya ta sanar da shirinta na kara kayan aikin samar da iskar Gas da kuma rage kudin sufirin na iskar Gas, zuwa kaso 40 a cikin dari.
Ta bayyana haka ne a yayin da aka rattaba hannun yarkejeniya ta shirin da aka gudanar a Abuja.
- Sin Na Adawa Da Kara Haraji Da EU Ta Yi Kan Motoci Masu Aiki Da Lantarki Kirar Sin
- Dimokuradiyyar Jama’a Da Ta Shafi Matakai Daban Daban Wani Muhimmin Tabbaci Ne Ga Ci Gaban Kasar Sin
A taron rattaba hannun yarjejeniyar, ya samu halartar masu ruwa da tsaki a fannin samar da iskar Gas da kuma wasu wakilan kungiyar kula da surin motoci NURTW da suka fito daga tashoshin motoci na Itakpe, Adabi, da kuma wakilan tasoshin Jiragen kasa da suka fito daga tashar Ajaokuta ta jihar Kogi.
Daraktan shirin samar da iskar Gas na fadar shugaban kasa Michael Oluwagbemi, a yawabinsa ya jaddda kokarin da gwamnatin tarayya ke ci gaba da yi wajen samar da saukin sufuri duba da tashin farashin man fetur.
“ A saboda haka ne, shugaban Bola Ahemd Tinubu ya kirkiro da shirin yin amfani da iskar Gas, mai makon dogaro da yin amfani da man fetur a fannin yin sufuri”.
Ya ci gaba da cewa, a cikin sabon shirin, kudin sufuri na motar haya da ke daukar matafiya takwas, an rage kudin sufurin daga Naira 12,000 zuwa Naira 7,000.
Kazalika, kudin sufurin motar haya da ke daukar matafiya hudu daga Abuja zuwa tashar Jirgen kasa ta Ajaokuta, an rage kudin sufurin daga Naira 13,000 zuwa Naira 8,000, inda ya kara da cewa,tsadar sufuri daga tashar Itakpe zuwa Warri, ta kai Naira 5,000, wanda hakan zai sanya matfiyi ya samu ragin kaso sama da 40 a cikin dari.
Ya ci gaba da cewa, domin a samu nasarar tura iskar Gas din, tuni a kafa cibiyoyi guda goma a Abuja, Itakpe, da kuma a Ajaokuta, ciki har da a tashoshi shida da hukumar mai ke tafiyar da su da kuma guda biyu a NIPCO.
Ya sanar da cewa, ana kuma shirin yin hadaka da tashshi da dama, wanda tuni, aka yi hadaka da kamfanin Bobas, domin a samar da karin kayan aiki a Abuja.
Oluwagbemi ya kara da cewa, kamfanin Greenbille na shirin kaddamar da karin wasu tashohi 17 a daukacin tashoshin da ke a kasar a karshen wannan shekarar.
“ Mun kuma yi hadaka da kafanin makamshi na Matrid Energy don a kafa wasu sabbin tashoshi biyar a jihar Delta da Abuja, tuni kamfanin NNPC, ya kammala aikin wasu tashoshi shida a Abuja, inda kuma ake jiran a kammala wasu shida a jihar Lagos nan da watan Okutoba”.
Ya ce, ana sa ran rage kudin sufurin, zai fara aiki ne a karshen watan Okutobar wannan shekarar.
A na sa jawabin, Sakataren kungiyar NURTW reshen tashar Ajaokuta Adeyemo Teslim, ya bayyana jin dadinsa a kan yin hadakar.