Gwamnatin tarayya ta cimma wasu matakai da ministoci za su gabatar da kwazonsu da suka iya cimmawa a ma’aikatunsu daban-daban, hakan kuma na cikin muhimman bangarori takwas da Shugaban kasa, Bola Tinubu ya sanya a gabasa.
Babban mai bai wa shugaban kasa shawara kan manufofi da tsare-tsare, Hajiya Hadiza Bala-Usman ce ta sanar da hakan a Abuja cikin makon nan.
- Sin: An Fitar Da Tsarin Tallafin Kudade Domin Bunkasa Ci Gaba Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba
- Liu Yuxi Ya Halarci Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kan Sin Da Afirka Karo Na Uku
Shugaban kasa ya shaida wa ministocinsa cewa tilas a kowace bayan wata uku su gabatar da kwazonsu domin sanin irin azama ko akasinsa da suke yi a bakin aikinsu.
Kazalika, gwamnatin Tinubu ta tsara da fitar da wani manhaja da zai bibiyar kwazon ministoci a ma’aikatunsu, manhajar mai suna ‘Citizens’ Delibery Tracker App’.
‘Yan Nijeriya za su iya amfani da manhajar wajen bayar da bayani ko ra’ayinsu kan manufofi da tsare-tsaren da gwamnati ke musu.
Sannan, hatta ayyukan mazabu da ake bai wa sanatoci da ‘yan majalisu za a dunga bibiya ta wannan manhajar.
Hadiza ta jaddada aniyar gwamnatin Tinubu na gudanar da gwamnati mai cike da gaskiya da fayyace komai ga al’umman kasa.
Ta ce, shugaban kasa ya umarci dukkanin ministoci da dunga zama da al’umman mazabun sanatocin yankunansu a kowace zango na bayan wata uku.
Ta take bayyana sabuwar salon mulkin Tinubu mai suna “Tsarin Mulki Na ‘Yan Kasa”, Hadiza ta ce, tun da dai ministocin nan sun rattaba hannun kan yarjejeniyar yin aiki tukuru, dole ne za a bibiyesu da tantancesu kan muhimman ajandoji guda takwas na Tinubu.
A cewarta, da wannan sabon dabarar bibiyar aikin za a samu cimma muhimman nasarori kan bangarori guda takwas da shugaban kasa ya sanya a gaba wajen ganin ya aiwatar domin kyautata rayuwar al’ummar Nijeriya.
A fadinta kuma, Tinubu ya amince al’umman Nijeriya su san dukkanin abubuwan da gwamnati ke yi da samun damar mu’amalar kai tsaye da ministoci domin himmar da yake da shi wajen gudanar da shugabanci na kwarai ga al’umman kasa.
Ta kara da cewa, sun kuma fito da tsarin gabatar da rahoton ayyuka da zai ba da dama ake samun hakikanin rahotonnin ayyuka da kwazon kowace ma’aikata da rassan gwamnati da kuma hukumominta.
“Muna rungumar tsarin gudanarwa ne na kasa da kasa domin kyautata shugabanci ta hanyar ganowa da bibiyar kwazon ma’aikatu a bangaren aiwatar da manufofi da tsare-tsaren gwamnati,” ta shaida.
Hadiza ta ce jama’an kasa za su iya samun manhajar bibiyar ayyukan da kwazon ne ta shafin yanar gizo kamar haka: app.cdcu.gob.ng.
Ta ce nan da wata guda za a dora manhajar a turakar ‘Google Play Store’ da ‘Apple store’, manhajar zai ba da dama jama’a su san masu kokari da akasin haka.
  Â