Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, ya amince da shirya babban taron girmamawa ga Nafisa Abdullah Aminu, ’yar shekara 17 da ta zama zaƙaƙurar duniya a fannin ƙwarewar Turanci a gasar TeenEagle Global Finals 2025 da aka gudanar a birnin London,da ke ƙasar Ingila.
Nafisa, ɗalibar makarantar Nigerian Tulip International College (NTIC), ta doke fiye da mutane 20,000 daga ƙasashe 69, ciki har da ƙasashen da ke amfani da Turanci a matsayin harshen uwa, lamarin da ya ja hankalin duniya ga ilimin Nijeriya.
- Gwamnatin Yobe Ta Rufe Kasuwanni Uku Saboda Fargabar Hare-haren Boko Haram
- Hadimin Gwamnan Yobe Ya Fice Daga APC Ya Koma Jam’iyyar ADC
Gwamna Buni ya bayyana nasarar Nafisa a matsayin wata babbar girmamawa ga jihar Yobe da Nijeriya baki ɗaya, yana mai cewa wannan nasara sakamako ne na zuba jari da gwamnatin sa ke yi a fannin ilimi.
A cewar sanarwar da Mamman Mohammed, Daraktan yaɗa labarai na Gwamnan ya fitar, Nafisa na daga cikin ɗaliban da ke amfana da tallafin karatu daga gwamnatin jihar Yobe, wadda ta riga ta tallafa wa sama da ɗalibai 40,000 a matakin jami’a da sauran manyan makarantu a cikin gida da waje.
Gwamnan ya bayyana cewa za a gudanar da babban taron girmamawa ga Nafisa a faɗin jihar, sannan ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ci gaba da gyaran makarantu da ɗaukar malamai domin ganin kowanne yaro a Yobe ya samu ingantaccen ilimi kamar Nafisa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp