Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya jaddada damuwar gwamnonin yankin kan yadda matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a yankin, ya kuma jaddada kudurinsa na hada kai da masu ruwa da tsaki don magance matsalar yadda ya kamata.
Gwamnan ya tabbatar da hakan ne ranar Litinin yayin da ya karbi cikakken rahoton Gamayyar Kungiyoyin Arewa (CNG) wadda kwamitin kwararru kan matsalar tsaro a Arewacin Nijeriya ya hada a wani bangare na sakamakon taron tattaunawa da aka gudanar kan matsalar a Abuja.
- Kakakin Ma’aiktar Tsaron Sin Ya Gabatar Da Yadda Aka Gudanar Da Atisayen Hadin Gwiwa Na Sojojin Sin Da Tanzaniya Da Mozambique
- Ƙaramin Ministan Tsaro Da Manyan Shugabannin Soji Sun Isa Sokoto Domin Fatattakar ‘Yan Bindiga
Yahaya ya ce rashin tsaro na kara tabarbarewa da rayuwar miliyoyin ‘yan Nijeriya, musamman a fannin noma, lamarin da ya janyo tashin farashin kayan masarufi ba a jihohin Arewa kadai ba, har ma da kasa baki daya.
Ya jaddada cewa gwamnonin sun dukufa wajen ganin sun magance matsalar rashin tsaron da ya addabi yankin, wanda ya haifar da cikas ga harkokin noma, ya kuma ta’azzara hauhawar farashin kayayyakin masarufi da kalubalen tattalin arzikin da kasar nan ke fuskanta.
Ya ce: “A matsayinmu na gwamnoni, mun damu matuka game da matsalar tsaro a Arewacin Nijeriya, wannan yanki ne da ya fi kowanne yawan al’umma a kasar nan, kuma yana da albarkatun ma’adinai da kasa mai dausayi don noma, karfin noman yankin yana taka rawar gani wajen samar da wadataccen abinci.
“Wani abin takaici shi ne, rashin tsaro da ake fama da shi a halin yanzu yana kawo cikas ga wadannan ayyuka, wanda ke haifar da tsadar kayan masarufi wanda kuma ya shafi dukkan ‘yan Nijeriya, ba kawai na Arewa ba.”
A wani mataki na tinkarar lamarin, kungiyar gwamnonin Arewa karkashin jagorancin Gwamna Inuwa Yahaya, ta bayyana shirin gudanar da wani taro da zai hada dukkan masu ruwa da tsaki da suka hada da shugabanni na da dana yanzu da sarakunan gargajiya da shugabannin tsaro da kungiyoyin fararen fula don tattaunawa tare da aiwatar da dabarun farfado da martabar yankin.
Gwamna Yahaya ya kuma yaba wa shugabannin gamayyar kungiyoyin na Arewa bisa cikakken nazarin da suka yi, yana mai yaba wa da rawar da suke takawa wajen magance matsalolin da yankin ke fuskanta.
Da yake jawabi tun farko, shugaban tawagar kuma shugaban kwamitin kwararru kan harkokin tsaro na kungiyar ta CNG, Bashir Yusuf Ibrahim, ya bayyana cewa rahoton da aka gabatar wa Gwamna Yahayan, sakamako ne na dogon nazarin da aka yi, duba da sassauyawar da ake samu na kalubalen tsaro a Arewacin Nijeriya don samar da hanyoyin magance matsalar.
Da yake karin haske kan wasu abubuwan da rahoton ya kunsa, Bashir ya bayyana wajibcin damawa da kowa wadda kungiyar ta bullo da shi don samar da hadin kai tsakanin masu ruwa da tsaki a sassan Arewacin Nijeriya don magance matsalar rashin tsaro.
Ya ce tuni kungiyar ta mika wannan rahoto ga Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ta ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro don daukar mataki a kai.
Da yake yaba wa da zaman lafiya da kwanciyar hankalin da ake samu a Jihar Gombe, jagoran tawagar ya bayyana cewa babu wata jiha da ta tsira daga miyagun laifuka matukar sauran jihohin suna fuskantar matsalar aikata laifuka.