A yau mun kawo Da farko za mu so sanin cikakken sunanki da tarihinki?
Suna na Sa’adatu Hussaini haifarfiyar ‘yar Hadejia ce na taso a garin Hadejia na yi karatu a garin Hadejia
- Yaki A Hukumance Da Matatar Dangote Da `Yan Nijeriya
- Arafat: NAHCON Ta Jagoranci Yi Wa Kasa Addu’a
Shin Sa’adatu matar aure ce?
A’a bani da aure amma an kusa insha Allahu.
Malama Sa’adatu ‘yar kasuwace ko ma’aikaciya ce?
Ni ma’aikaciya ce sannan kuma ‘yar kasuwace ina dan tabawa.
Wanne irin aiki kike yi?
Ni ma’aikaciyar lafiya ce.
Ma’aikaciyar lafiya kamar a wanne fanni?
Ni ina laibo rum wato in fanni karbar haihuwa.
Ya matsalolin da kuke fuskanta wajen huihuwa?
Wannan maganar gaskiya ne zaki ga wata ta zo haihuwa amma ta kasa da kanta dama a cikin shirin kayan aihuwa idan aka shiga da mai haihuwa lebo rum kayan da zaka hada dama akwai kayan da idan mai haihuwa ta kasa haihuwa da kanta za a yi mata aiki, dama zaki ga wata sai haihuwar tazo gaf sai kiga an samu matsala ta kasa to dama za mu duba idan akwai wani taimako da za a yi ta haihu sai ayi idan kuma aiki ne sai ayi.
Malama Sa’adatu su wadannan wadanda basu da kukun haihuwa tayaya kuke ganesu?
Daga haihuwa farko ake gane macen da bata da kukun haihu idan kika zo haihu haihuwar ta gagara sai aduba a gani kina dashi to tanan ake ganewa. Dama a jikin mace tanada koku guda uku ne da na farko dana biyu na kuna na uku wanda shi ne na karshe to wannan na karshen idan ya zamana shi karami ne to mace ba za ta taba iya haihuwa da kanta ba.
To ya kuke ji idan mai haihuwa ta zo haihuwa idan ya zo da karar kwana rai ya yi halinsa?
Gaskiya babu dadi zaki ji ranar kwata-kwata kin zama kamar wata marar lafiya saikiga kamar kin gagare aikin ki ne duk mai rai zai dandana mutuwa sannan kuma ita lokacin tane ya yi kuma wannan haihuwa shi ne ajalinta to babu yadda ka iya, wata zaki ga bawai haihuwar fari bace ba kuma ta biyu ko uku ba wata haihuwar ma can danisa ce to tanan sai kagane lokacinta ne ya yi sai ka yi imani da kaddarar haka.
To a kan samu wadda danne yake rasuwa yabar uwar to shima ya kuke jin wannan?
Shima babu dadi ana murna za a samu karuwa zaki ga ga wata uwar sai ya baki tausayi sai dai mu yi ta basu hakuri harma idan haihuwar fari ce gaskiya babu dadi, wani zaki ga nace kusan uwar ita ke kashe danta da kanta saboda sai ku yi ta fama dasu a kan su buda kafafuwansu amma ina sai kana ta kokarin bankarasu suna komawa to wani a haka ake samun yaro ya rasu.
Malama Sa’adatu me ya ja hankalinki da har kika tunani yin wannan karatu?
Saboda ni macece inaso ace mata munyawaita wajen bangaren karbar haihuwa.
To ya kikaji da gwagwaryamar karatun likita wasu suna cewa akwai wahala gashi ke harkin gama kina aiki?
Alhamdulillah karatu kam akwai wahala sosai ma karatun likita sai anjure saboda zakiga ko kwas daya ba’aso ki fadi duk anaso ki addaceshi a jikin kwakwalwarki.
Sa’adatu baki fada mana matakin karatun kiba?
Na gama jami’a
Wanne irin kalubale kika taba fuskanta wajen karatu ko aikinki?
Gaskiya akwai kalubale masu yawa awajen karatu da aikina kowa yasan yanda yanayin aikinnamu yake sai dai hakuri.
Zuwa yanzu wanne irin nasarori kika cimma?
Shi kansa aikin da nake nasara ce a waje na saboda na cimma burina bayan haka nacimma abubuwa da dama arayuwata.
Wanne abune yafi farantamiki rai acikin aikinki?
Idan na gamu da marasa lafiya zakiga suna shima mutum albarka.
Dame kike so mutane su riga tunawa dake?
Jajir cewa ta akan aikina da kuma tausaywa marar lafiya.
Wanne irin addu’a ne idan akayi miki kike jin dadi?
Idan akace Allah yajikan magabata na.
Wanne irin goyan baya kike samu wajen iyaye da ‘yan uwa?
Gaskiya ina samun goyan baya sosai
Kawaye fah?
Eh gaskiya kawaye na suma suna goya mun baya dari bisa dari.
Me kika fiso acikin kayan sawa?
Nafi son abaya
A karshe wanne irin shawara zaki ba ‘yan uwanki mata ?
Ina so na basu shawara a kan su tashi su yi karatu domin taimaka wa mata ‘yan uwanmu ta hanyar lafiya ki taimaka wa al’umma kuma kema zaki taimaki kanki.