Adams Oshiomhole fitaccen ɗan siyasa ne a Nijeriya, kuma Tsohon Gwamnan Jihar Edo. Yanzu haka, shi ne Sanatan da ke wakiltar Edo ta Arewa. Jagoranci da ƙwarewarsa a fannin siyasa sun taka rawar gani sosai a siyasar Nijeriya, musamman a zaɓen Gwamnan Jihar Edo na 2024, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar ɗan takarar Jam’iyyar APC, Sanata Monday Okpebholo.
An haifi Oshiomhole a ranar 4 ga watan Afrilun 1952, a Jihar Edo. Ya fara aikinsa a matsayin mai fafutukar kare haƙƙin ma’aikata, inda ya zama Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC). A lokacin da yake shugabancin NLC, ya tsaya tsayin daka wajen kare haƙƙin ma’aikata, ya kuma jagoranci tattaunawa kan muhimman manufofi, wanda ya sa aka san shi a matsayin jagora mai tsayin daka.
- Ɗangote Ne Gwarzon Jaridar LEADERSHIP Na Shekara Ta 2024
- Gwarzon Gwamnan Shekara Ta 2024: Alhaji Abba Kabir Yusuf
A shekarar 2008, ya zama Gwamnan Jihar Edo, bayan hukuncin kotu. A lokacin mulkinsa, ya mayar da hankali kan inganta ababen more rayuwa da kiwon lafiya da ilimi, ciki har da shahararren shirinsa na “Red Roof Revolution,” wanda ya gyara makarantu a faɗin jihar. Salon mulkinsa na kula da jama’a ya sa ake girmama shi sosai.
A shekarar 2018, an naɗa shi shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, inda ya tallafa wa jam’iyyar kuma ya goyi bayan gwamnatin Shugaba Buhari. Duk da ƙalubalen cikin gida, jagorancin Oshiomhole ya taimaka wajen samun nasarori a zaɓuɓɓuka masu muhimmanci.
A matsayinsa na Sanata, ya mayar da hankali kan ci gaban ababen more rayuwa, bai wa matasa dama, da samar da ayyukan yi mazaɓarsa. Har yanzu yana da tasiri a wajen al’amur ƙasa da na yankinsa, inda yake amfani da ƙwarewarsa a fannin mulki da fafutuka.
Sadaukarwar Oshiomhole wajen yi wa jama’a hidima da rawar da ya taka a fagen siyasar Nijeriya ya sa ya cancanci zama Gwarzon Ɗan Siyasa na Shekarar 2024 na Jaridar Leadership.
Tsarin shugabancinsa na samar da ci gaba da bai wa al’umma ƙwarin gwiwa yana matuƙar tasiri a ƙasar nan.