Barrister Nyesom Ezenwo Wike, wanda aka fi sani da “Mr. Project”, ya samu lambar yabo ta Jaridar LEADERSHIP saboda irin gudummawarsa wajen samar da ci gaba ta hanyar samar da ababen more rayuwa ga al’umma a yankunan karkara da birane.
A matsayinsa na ministan babban birnin tarayya, ya kawo sauye-sauye masu yawa, wanda hakan ya sa ya zama jagora mai hangen nesa da jajircewa.
Tarihi da Karatunsa
An haifi Wike a garin Rumuepirikom, Obio-Akpor da ke Jihar Ribas, a ranar 13 ga Disamba, 1967. Ya karatu a sakandaren gwamnati a Eneka, daga nan ya shiga Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Ribas (RSUST), inda ya samu digiri na farko a fannin Shari’a (Law). Bayan haka, ya halarci makarantar koyon aikin lauya (Law School) a shekarar 1997, kuma daga bisani ya samu digiri na biyu a Siyasa da tsare-tsare (Political and Administrative Studies) daga wannan jami’a.
Shigarsa Siyasa
Wike ya shiga harkokin siyasa a 1999, lokacin da ya zama shugaban ƙaramar hukumar Obio-Akpor, wanda ya yi shekaru takwas yana mulki. Daga bisani ya zama Shugaban ma’aikata na gwamna Rotimi Amaechi. A shekarar 2011, an naɗa shi ƙaramin Ministan Ilimi a ƙarƙashin gwamnatin Goodluck Jonathan, inda ya kai matsayin Ministan Ilimi mai cikakken iko a 2013.
A matsayinsa na minista, ya kawo sauye-sauye masu mahimmanci a tsarin ilimi a Nijeriya. Ya kuma jagoranci sauyin manufofin da suka inganta damar samun ingantaccen ilimi a duk faɗin Nijeriya.
Gwamnan Jihar Ribas
A ranar 29 ga Mayu, 2015, Wike ya zama Gwamnan Jihar Ribas, inda ya gudanar da ayyukan ci gaba masu tarin yawa. A cikin shekaru takwas na mulkinsa, ya gabatar da ayyukan gine-gine da samar da hanyoyi da inganta lafiya da kuma haɓaka ilimi. Ya kuma tabbatar da biyan albashin ma’aikata akan lokaci da biyan kuɗaɗen ‘yan fansho da tsofaffin ma’aikata. Ya ƙaddamar da ayyukan da suka shafi rayuwar mutanen jiharsa masu muhimmanci, ciki har da samar da hanyoyin mota da gadaje da titunan a birane da karkara. Wannan ya sauya fuskar Jihar Ribas, hakan ya sa al’umma suka amince da jagorancinsa.
Matsayin Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT)
An naɗa Wike a matsayin ministan babban birnin tarayya (FCT) a ranar 16 ga Agusta, 2023. Da hawansa wannan matsayi, ya yi duba na musamman kan ayyukan da aka fara amma ba a kammala ba a Abuja. Ya gano manyan matsaloli, musamman waɗanda suka shafi rashin isassun kuɗaɗe, sannan ya ɗauki matakan gaggawa don magance su.
A matsayinsa na minista, Wike ya tabbatar da shugabanci mai kyau wajen bayar da kwangiloli, yana mai cewa ba zai bayar da kwangila ba, ba tare da an tabbatar da kuɗin da ake da su ba a ƙasa ba. Wannan ya kawo gaskiya da inganci a tsarin gudanarwa. Ya gina hanyoyi,
da asibitoci da makarantu a sassa daban-daban na Abuja, ya kuma tabbatar da cewa kowanne yanki ya amfana da shugabancinsa.
Haka kuma, ya sake farfaɗo da filin jirgin saman Abuja na biyu, wanda ya kawo sauƙi ga zirga-zirgar jiragen sama. Ya kuma samar da ingantaccen tsarin sufuri wanda ya rage cunkoso da bunƙasa kasuwanci a Abuja.
Walwalar Ma’aikata da Aikace-aikace
A ƙarƙashin jagorancinsa, Wike ya tabbatar da biyan albashin malaman makaranta da sauran ma’aikata da ya gada a matsayin bashi. Har ila yau, ya inganta walwalar ma’aikata ta hanyar ƙarawa sama da 1,000 girma, wanda hakan ya ƙara musu kwarin gwuiwa. Wike ya tabbatar da cewa ya bai wa sha’anin tsaro fifiko, inda ya haɗa kai da hukumomin tsaro da ƙungiyoyin sa kai don tabbatar da zaman lafiya a Abuja. Wannan ya rage yawan laifuka a birnin, kuma ya ƙara ƙwarin gwuiwar jama’a kan aikin hukumomin tsaro.
Salon Jagorancinsa
Kowa ya san Minista Wike, gwani ne wajen bai wa jama’a kula. Yana ziyartar wuraren gudanar da ayyuka, yana sauraron ƙorafe-ƙorafen jama’a, sannan yana tabbatar da cewa an magance matsalolin da suka taso cikin ƙanƙanin lokaci. Wannan salon jagoranci ya sa jama’a suka gamsu da da irin shugabancinsa.
A yau, Minista Wike ya kafa tarihi a babban birnin tarayya ta fuskar aiyukansa na bunƙasa hanyoyin more rayuwa da walwalar jama’a da tsaro, wanda hakan ya tabbatar da cewa yana da hangen nesa da jajircewa wajen bunƙasa Abuja. Wannan lambar yabo tana nuna yadda ya ke amfani da jagorancinsa wajen kawo ci gaba mai ma’ana ga jama’arsa.