Ɗan wasan gaban Manchester City, Erling Haaland, zai ziyarci ƙwararren likita saboda rauni da ya samu a idon sahunsa a wasan da suka buga da Bournemouth a gasar kofin FA ranar Lahadi.
Duk da haka, ƙungiyar ta ce tana fatan Haaland zai warke a kan lokaci don ci gaba da wasa a wannan kakar.
- Allah Ya Yi Wa Galadiman Kano, Abbas Sanusi, Rasuwa
- Kasar Sin Mai Tabbatar Da Daidaito A Duniya Mai Cike Da Rashin Tabbas
A lokacin wasan, an cire Haaland a minti na 61 bayan ya zura ƙwallo guda.
City ta lashe wasan da ci 2-1, wanda ya ba ta damar zuwa wasan kusa da ƙarshe.
Bayan an yi masa gwaje-gwaje, an tura Haaland ga ƙwararren likita don duba lafiyarsa.
Ya kuma yi kuskuren bugun fanareti a farkon wasan kafin daga bisani ya zura ƙwallo guda.
A halin yanzu, kofin FA ne kawai gasar da ake ganin Manchester City na da damar lashewa a kakar bana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp