Connect with us

SIYASA

Hadin Kan Kansiloli Ne Sirrin Nasarar Karamar Hukumar Nasarawa

Published

on

Mai taimakin Gwamnan Kano Dakta Nasiru Yusif Gawuna wanda Kuma yanzu haka shi ne ke rike da mukamin Kujerar Gwamnan na wucin gadi, ya bukaci al’umma dasu rungumi zaman lafiya wanda shi ne sinadarin duk wani ci gaba da ake bukata, Mai rikon kujerar Gwamnan Dakta Nasiru Yusif Gawuna na yin wannan jawabin ne alokacin da ya karbi bakuncin Kansilolin Karamar Hukumar Nasasara wadanda suka kai masa ziyarar zumunci a ranar Lahadin data gabata.

Gawuna ya bayanna cewa baiwa shugaban karamar Hukuma dukkan goyon baya daga zababbun kansilolin  shi ne zai tabbatar da cikar burinsu na hidimtawa al’ummar da suka zabesu.

Yace  Karamar Hukumar Nasarawa ce Karamar Hukumar data zarta sauran Kananan Hukumomin Jihar Kano zaman lafiya, don haka ya bukaci dasu ci gaba da rike wannan kambu  domin samun Nasarorin da aka sa gaba.

Dakta Nasiru Gawuna  y ace duk da matsalar tattalin arziki,  Jihar Kano  karkashin Jagorancin Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta ci gaba da gudanar da manyan ayyuka tare da tabbatar da biyan albashin ma’aikata akan lokaci. A cewar Mataimakin Gwamnan  wani lokaci a baya sai Gwamnatin Jiha ta tallafawa Kananan Hukumomi kafin su iya biyan albashi, ya yinda wasu Jihohin  suka gaza sauke irin wannan nauyin albashin ma’aikata.

Dakta  Nasiru Yusuf  ya ci gaba  da cewa Gwamnatin Ganduje na bayar da dukkan hadin kai ga kananan Hukumomin Jihar Kano 44 domin su samu damar gudanar da ayyukanraya kasa a yankunansu.

Tunda farko da yake gabatar da Jawabinsa a madadin Kansilolin Alhaji Sale Musa Shu’aibu wanda kuma shi ne kakakin Majalisar Kansilolin Karamar Hukumar Nasarawa, yace sun ziyarci Mataiakin  Gwamnan ne a gidansa domin taya shi murna  bisa  nadin da  Gwamna Ganduje ya yi masa amatsayin mataimakin Gwamna.

Don haka a madadin daukacin mambobin wannan Majalisar  karamar Hukumar Nasarawa,  ina gabatar da taya murna ga Dakta Nasiru Yusif Gawuna, gimshikin cigaban al’umma kuma nagarataccen jagora bisa wannan zabin cancanta da akayi maka na mataimaiin Gwamna Kano.

Alhaji Sale Musa Shu’aibu ya yi addu’ar fatan Allah ya ci gaba da taimakon Gawuna zamansa a wannan mukami, Allah ya kara masa karfin guiwar taimakawa Gwamna Ganduje wajen daukaka kimar Jihar Kano. Kamar yadda Mai Magana da yawun Mataimakin Gwamnan Malam Hassan Musa Fagge ya shaidawa LEADERSHIP A Yau

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: