Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta umarci dukkan maniyyatan hajjin bana su tabbatar da sun biya akalla Naira miliyan 4.5cikin makwanni 3 saboda cimma sabbin tsare-staren da hukumar kasar Saudiya ta fito da su a wannan shekarar don ganin an samu nasarar aikin hajin bana tare da tabbatar da inganta jin dadin alhazai a yayin da suke a kasa mai tsarki. Wannan umarni ya tayar da hankulan al’umma masu miyyar saike farali a shekara mai zuwa.
Wannan na faruwa ne ganin yadda ake fuskantar radadin kuncin matsalar tattalin arziki da al’umma ke fuskanta sakamakon karyewar darajar Naira a kasuwar bayan fage. Wakilinmu ya tattauna da wasu maniyya a kan yadda suka karbi wannan wa’adin da kuma yiwuwar cika wannan wa’adi kamar yadda hukumar alhazai ta bayyana.
- Hajjin Badi: Dalilin Kara Kudin Kujera Zuwa Naira Miliyan 4.5 – NAHCON
- Hajjin 2023: NAHCON Za Ta Kammala Dawo Da Alhazan Nijeriya A Watan Agusta
Wata maniyyaciya mai suna Habiba Muhammad da ke da zama a anguwar Sanusi a Jihar Kaduna ta koka a kan waa’din na mako uku kacal da hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON ta bai wa maniyyatan na su zuba Naira miliyan 4.5 a cikin asusun gata. Ta ce, akwai matukar bukatar hukumar ta sake yin tunani a kan wannna wa’adin na ta, duba da yadda ake a cikin karancin kudi saboda halin kuncin rayuwa da wasu alummar kasar ke fuskanta.
Kazalika ta bayanna cewa, ita manomiya ce, kuma a yanzu tana ajiye da kimanin Naira miliyan uku ne a asusun bankin da take ajiya, musamman domin ita ma ta je ta sauke faralin, ganin cewa, ba ta taba zuwa aikin hajji a rayuwarta ba.
Shi ma wani maniyyaci Sani Lawal mazaunin yankin mahuta a Jihar Kaduna, ya yi nuni da cewa, wannan wa’adin na hukumar NAHCON, ya zo mashi a matsayin bazata.
Lawal ya yi nuni da cewa, idan mahukuntan hukumar aikin hajin ta kasa ba wai suna so ne, mu je sauke faralin mu ba ne, ko kuma suna da wata manufa a zuciyarsu da suke son cimma buri, me ya sa suka sanar da wa’adin a cikin gaggawa.
Shi kuwa wani maniyyaci mai suna Kabir Ashiru da ke zaune a anguwar Tudun Wada Kaduna ya sanar da cewa, ba tun yau ake fusknatar dimbin kalubale a harkar aikin hajji na kasar nan.
Ya yi nuni da cewa, ikirarin da hukumar ta yi na cewa, dalilan da suka sa ta bayar da wannan wa’adin na ajiye Naira miliyan 4. 5 a asusun gata, don guadanr da shire-shiryen aikin hajjin a kan lokaci, amma ko a aikin hajji na bana, an samu dimbin matsaloli duk da cewa maniyatan na bana sun biya kudadensu a kan lokaci, hatta a gun ita hukumar ta kasa wajen jigilar maniyyatan zuwa Saudiyya da kuma kwaso su daga Sasudiiya zuwa gida Nijeriya.
Ita kuwa wata maniyyaciya da ke zaune a Kurmin Mashi a Kaduna a na ta ra’ayin ta ce, wannan wa’adin zai yi wuya akasarin maniyyatan da ke son zuwa Sadiyya yin ibadar su iya cika shi.
A cewarata, a yanzu, ta tara Naira miliyan biyu ne kawai a asusun ajiyarta na bankin don zuwa yin ibadar, amma wannan wa’adin na hukumar, ya karya mata kwarin guiwa.
Ta ce, ganin cewa Saudiyya ta ware wa Nijeriya kujeru guda 95,000 don maniyyata su tafi kasar yin aikin hajji anma saboda wannan wa’adin, na hukumar zai yi matukar wuya a Nijeriya ta cimma wannan adadin.
Ta yi kira ga shugaban kasa da masu ruwa da tsaki a kasar da su sa baki don hukumar ta sake yin tunin akan wannan wa’adin in har ana son Musulman da ba su taba zuwa aikin hajjin ba suma su samu ikon zuwa.
Domin jin ta bakin hukumar alhazai NAHCON, Mataimakin Editanmu ya tattauna da Kwamishinan Kula da Ma’aikata da Kudi a Hukumar Alhazai ta Kasa, Alhaji Nura Hassan Yakasai, inda ya yi bayani a kan yadda biyan kudin a kan lokaci zai tabbatar da gudanar da aikin hajji cikin nasara.
Ya kuma bayyana cewa, “Ba kwanan nan ba ne, kusan tun ‘Meeting’ din da muka yi wajen sati hudu da ta wuce tare da manyan sakatarorin jin dadin alhazai na jihohi. A lokacin muka yi taro da su baki daya cewa, muka tabbatar da ya kamata maniyyata na shekara mai zuwa 2024 su ajiye kudin ajiya kamar kafin alkalami. kuma nawa ya kamata? A wannan taron ne aka yarda cewa ganin yadda darajar Naira ke faduwa a kullum, ya kamata a sanya Miliyan hudu da rabi lokacin da aka samu kudin aikin hajji aka fito dashi sai ya zama ciko da ake ba wani sabon biya za a sake ba. Muna kyautata zaton kudin nan sai ya kai wajen miliyan 5. Ka ga idan mutum ya biya hudu da rabi ka ga ciko zai yi. Yayin da ake ce ka biya hudu da rabi ko miliyan biyu aka zo aka ce ka cika miliyan daya ka fi karfin ciko sabon biya kenan. An yanke wannan shawarar nedon tafi bai daya gaba daya da dukkan jihohin tarayyar Nijeriya. Maimakon a ce wasu jihohi suna karbar kudin kafin alkalami na miliyan biyu wasu na karbar miliyan hudu da sauran su, gara a ce, duk an tafi bai daya, musamman kuma ga sh lokaci na ta tafiya”.
Ya kara da cewa, “A kan haka muka sake fitowa da ita dokar domin tunatar dasu hukumomin alhazai cewa abin da aka yarda a wannan taron shi ne miliyan hudu da rabi. Sannan kuma lokacin da aka yana matsowa, don ana son a lokacn da aka shiga sabon shekara ya zama sauran cikon da maniyyati zai babu yawa, musamman ganoin hukumar kasar Saudiya na dson fara bayar da Bisa ne a cikin watan Ramadan”.
Da aka tambaye shi bambancin wannan stari na wannan shekarar da yadda ek yi a baya, Alhaji yakasai ya ce, “Banbancin kamar yadda na fada ma, hukumomin Saudiyya sun fito da suna da jadawalin yadda suke so aikin hajji na shekara mai zuwa ya kasance. Sai dai babban canji da suka fito dashi wanda ba a saba dashi ba shi ne suna so a yi wa dukkan baki daya al’umma da za su je aikin Hajji na wannan shekarar BISA kafin kwana hamsin da hawa Arafa. Watakila sun fito da wannan ne saboda matsalar da aka samu a masha’ir na wannan shekarar suma suna so su tabbatar da cewa alhazai nawa ne za su zo daga kowace kasa su samu lokaci koda wata biyu kenan su shirya ganin haka ne ya sa dole cewa mu sanar da maniyyata na shekara mai zuwa cewa su biya kudi da sauri sauri kafin wannan lokacin toh shi yasa aka ba da wato daga nan zuwa biyar ga watan Fabrairu Insha Allahu”.
Ya kuma nuna jin daddinsa a kan yadda maniyyata suka karbi wanna sabon tsarin, ya kuma ce, “Kowa ya sani halin da ake a cikin kasar kuma game da yadda darajar Naira ta shafi komai a rayuwar al’umma ciki harda aikin hajji. Toh na farko dai sun gane cewa shi kan shi miliyan hudu da rabi an sa ne ya zama kamar kafin alkalami.
Sannan na biyu kuma mun masu bayani kuma za a ci gaba da bayani don yanzu muna shirye-shirye, za mu yi amfanio da hanyoyi daban daban wajen wayar da kan al’umma a kan wannan shirin saboda tsarin da ita hukumar Saudiyya ta kawo na cewa in ya rage saura kwana hamsin a hau Arfa za a rufe yin BISA. Toh ya zama dole kenan kowani maniyyaci wanda yake so ya yi aikin shekara mai zuwa ya biya kudin shi ko kuma wannan kudin ajiyar kafin wannan lokaci”.
Daga karshe ya kara da cewa, “Kullum ana kawo tsare-tsare wanda za su sha banban da na kowane shekara musamman daga su hukumomin Saudiyya, kuma wannan shekara ta zo daban da a kan yadda aka saba yi, za ka ga wani lokacin maniyyatan ba sa gama biyan kudinsu sai an gama azumi. Saboda ana so a gama BISA kusan cikin azumin saboda haka ya kamata duk wanda yake da niyyar zuwa aikin Hajji ya yi kokari ya biya wannan kudin. Sannan kudi da aka sa miliyan hudu da rabi an sa sune saboda halin da Naira take ciki amma daga nan zuwa lokacin da za a ayyana kudin aikin Hajji in Allah ya sa Naira ta kara daraja toh sai a samu sauki a kan wannan” in ji shi.