Daya daga cikin manyan matasan Malamai a Jihar Kano, kuma shugaban kungiyar masu ilimin taurari na Afrika, Sheikh Muhajjadina Sani Kano.
Ya yaba da yadda hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) ta jagoranci gudanar da aikin hajjin bana, ya kuma nemi su kara kaimi wajen bunkasa jin dadin alhazai a shekaru masu zuwa Ya yi wannan bayani ne a tattaunawarsa da manema labarai bayan kammala aikin hajji na wannan shekarar.
Ya kuma kara da cewa, “An gudanar da aikin Hajji bana cikin koshin lafiya Alhamdulillahi gaskiya. Da yawa mutanen mu ‘yan kasar mu Nijeriya suna cikin kwanciyar hankali da kuma da a sun gudanar da aikin su cikin da a da kwanciyar hankali ba tare da wani rigima ko fadace-fadace ba ko sace-sace ko wani abu da zai tada hankali ko da zai zubar mana da mutuncin kasa, Alhamdulillahi gaskiya na gudanar da aikin Hajji cikin koshin lafiya.
Duk da dai ba a rasa yan kura-kurai da ba a rasa ba amma dai alhamdulillah hajjin bana sai dai cika ta yi cika an cika an cika sosai sosai kwarai da gaske dan Adam ba a magana an cika kuma kowa yana cikin walwala an gabatar da aikin Hajjin bana Alhamdulillahi’’.
- An Nemi ‘Yan Nijeriya Su Ba Shugaba Tinubu Goyon Baya
- Ba Zan Amince Da Cin Mutunci Da Yi Mani Zagon Kasa Ba – Shugaban NPA, Bello Koko
Ya kuma shawarci hukumomin alhazzai da su kara zage damstse wurin kokarin tallafa wa mahajjatan su na kowane jiha.
‘Yan matsaloli da a ka riga a aka samu bai wuce matsaloli na bata da a ke samu na alhazai ba ko dattijai ka ga dattijuwa ko dattijo ya bata bai san ina zai je ba bai san ina yake ba yana ta tangalili a filin aikin Hajji a filin Arfa a Minna ko in yaje jifa ya rasa ma ina zai yi ko in ya zo Makka harami kaga ya rasa ina ne masuakin shi ma.
Toh shawarar da zan riga in basu bata wuce yana da kyau a ce a Minna su kara wakilai sun yi kadan gan ‘welfare operation’ sun yi kadan gaskiya a kara yawan su sannan yana da kyau a ce a Makkah kusa da harami ko bakin harami ace nan ma suna da wakilai kowacce Local gobernment tana da wakilanta daga kowace jiha idan Alhaji ya bata ya zamana a nan akwai wakilai don a nan suka fi bata za a zo an sa inda wakilai suke za su damka su hannun kowani wakili shi kuma zai san ina kake daga ina kake tun da Kowane da ID card din shi da tag din shi a hannu zai san ina kake daga ina ka fito za je ya damka ka masaukin ka wasu alhazan sun bata akan titi suke kwana ni kai na nan da yawa da yawa da yawa da yawa na ga wadanda sun bata ko ni na taimakawa wasu gurin nemo masu masaukan su ko in nemo shuwagabannin su na wannan jiha in damka su hannun su toh yana da kyau a ce an tsara wannan a gyara wannan abu.