Hamma: Dabi’ar Da Ta Gagari Masana

A shekarar 1986, wani likita mai suna Dakta R. Probine ya bayyana cewa, “Ya zuwa yanzu, babu wata dabi’a da dan adam ke aikatawa, wacce a ka kasa fahimtarta kamar hamma”

Daga wancan zance na Dakta R. Probine zuwa yanzu shekaru 30 ne cur, amma ba a iya gano hakikanin abin da ke sabbaba wannan dabi’a ba a kimiyyance. Sau da yawa idan an yi maganar hamma, a na kawo sababinta ta dayan uku, alamar jin bacci, damuwa, rashin wadatacciyar iska a jikin mutum.

A mafi yawan lokuta, da zaran mutum ya yi hamma, sai a ce ya na jin bacci ne, bisa la’akari da a ka yi na cewa a na yawan yin hamman ne a kafin a fara bacci da kuma bayan an farka daga bacci.

A na danganta hamma da gajiya ne, saboda da zaran mutum ya gaji yayin gudanar da wani aiki ko ya jima a zaune, zai rika yin hamma sosai. A kan wannan ne a ka gudanar da wani bincike, wanda a ka raba dalibai gida biyu. Kason farko a ka sa suka yi ta kallon wani zane na tsawon mintuna 10, kaso na biyu kuma a ka sa suka kalli bidiyon waka na mintuna 30. Daga karshe, sai ya zama masu kallon zane na mintuna 10 su ne suka fi yin hamma. Saboda su ne suka gaji da abin da su ke aikatawa.

A bangaren rashin wadatacciyar iska kuwa a jikin mutum, akwai wadanda ke cewa mutum na yin hamma ne domin ya samu wadatacciyar iskar da za ta rika yawo a kwakwalwarsa. Wanda wasu masana kimiyya suka musanta yiwuwar wannan hasashe.

A shekarar 2010, wani likita mai suna Adrian Guggisberg ya kara jaddada cewa hamma ta na da alaka da karancin iska a jikin mutum, musamman ma a kwakwalwa.  Sai dai likitan bai bayar da tabbaci a kan hasashen na shi ba a matsayin shi ne dalilin yin hamma da mutane ke yi.

Tambayar a nan ita ce, shin da gaske hamma na taimakawa kwakwalwa wurin yin sanyi? Wasu masanan sun tafi a kan cewa eh haka ne. Akwai wadanda suka ce idan mutum ya dora kankara ko ruwan sanyi a kansa, har ya cire ba zai yi hamma ba. saboda a wannan lokacin kankarar ko ruwan sanyin na sanyaya kwakwalwa, don haka ba ta bukatar hamma domin ta yi sanyi.  A daya bangaren kuma, wasu masanan sun ce yanayin da a ke ciki ne ke sa a rika yawan hamma. An fi yin hamma a lokacin da zafi ya tsananta fiye da lokacin sanyi.

Har zuwa yanzu dai masana sun kasa fitar da wani sakamakon bincike guda daya wanda ke tabbatar da dalilin samuwar hamma. wasu masu binciken sun ce a na yin hamma ne domin a fitar da iska marar amfani daga hunhu, saboda hunhu ya tsira daga cutar da suka kira ‘Atelectasis’.

A ‘yan kwanakin baya wasu masanan sun ce ba zai yiwu a kimiyance a fitar da dalilin sakamakon hamma ba, sai dai a danganta al’amarin ga dabi’a, wanda masana halayyar dan Adam da zamantakewa ne za su iya bincike su samar da dalilin samuwarta. Wannan na nufin kenan za a kalli ita kanta dabi’ar a mabambantan al’ummu a ga menene ke haifar da ita a wurinsu. A wanne yanayi mutane ke hamma, ko kuma me ke haifar mu su da afkuwarta?

Wani abin mamaki da hamma shi ne a dai dai lokacin da ka ga wani ya yi, zai yi wahalan gaske ba ka yi ba, ko kuma wani na kusa da kai bai yi ba. kuma a duk lokacin da ka ke tunanin hamma, zai yi wahala ba ka yi ta ba.

Wani abin mamaki da al’ajabi shi ne ba mutane ne kadai su ke hamma ba, hatta dabbobi ma sukan yi hamma. musamman dabbobi Birai irinsu Chimpanzee, Macakues, da Baboons. Sannan Karnuka ma sukan yi hamma. ka lura da kyau, idan ka na da Kare, duk lokacin da ka yi hamma, zai yi wahala bai yi ba.

Hamma dabi’a ce da ba za a iya kiranta da cuta ba ko mai cutarwa ga jikin dan Adam, sai dai kuma yawan yin hamman na nufin mai yi na fama da wata sigar rashin lafiya da ke bukatan ya je ganin likita. Wasu likitocin sun ce yawan yin hamma na da alaka da ko dai ciwon zuciya ko kuma matsala wacce ta danganci kwakwalwa.

Daga karshe, kamar yadda a ka kasa gano musabbabin wannan dabi’a a kimiyyance, wanda za a ce shi ne dalilin da ya sa a ke hamma, ba a rika kame – kame ba. haka nan har zuwa yau babu wani bincike guda daya daga masana halayya da zamantakewa da ke nuna dalili daya tilo da ke sabbaba hamma.

 

 

Exit mobile version