Mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng, ya gabatar da jawabi yayin babban taron mahawara na MDD na 81, a jiya Asabar 26 ga watan nan, a hedkwatar majalisar dake birnin New York na kasar Amurka.
Cikin jawabin nasa, Han Zheng ya ce yayin babban taron MDDr na 76, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da shawarar inganta ci gaban duniya ko GDI, kana daga bisani ya gabatar da shawarar inganta tsaron duniya, da ta inganta wayewar kan duniya, da ta kyautata jagorancin duniya, shawarwarin da suka samar da managarcin jagoranci wajen gina al’ummar duniya mai makomar bai daya ga daukacin bil Adama.
Kazalika, karin kasashe na nuna aniyarsu ta yin hadin gwiwa, da sauke nauyin dake wuyansu a tarihi, da fuskantar wahalhalu da kalubale, da kyautata walwalar bai daya ta dukkanin bil Adama.
Han Zheng, ya kuma gabatar da shawarwari guda hudu.
Na farko, ya ce akwai bukatar wanzar da odar bayan yaki, da gina yanayin zaman lafiya mai dorewa ta hanyar samar da tsaron bai daya.
Na biyu kuma, a tunkari matsalolin ci gaban duniya, da ingiza walwalar bai daya ta hanyar gudanar da hadin gwiwa a bude.
Na uku, a yayata musayar al’adu da koyi da juna, da gina hadin kai da aminci ta hanyar tattaunawa da shawarwari.
Na hudu kuma a daga matsayin cudanyar mabambantan sassa, da kare gaskiya da adalci ta hanyar aiwatar da matakai na hakika. (Saminu Alhassan)














