Ibrahim Muhammad" />

Harajin 7.5 Abin Alkhairi Ne Ga Cigaban Nijeriya – Mahmood Tauhid

An bayyana karbar karin haraji na 7.5 cikin 100 akan kayayyaki a kasar nan da cewa zai taimakawa bunkasar cigaban tattalin arziki, Shugaban Kamfanin hada-hadar harkar magungunan amfanin gona na Miagro, Alhaji Mahmood Tauhid ya bayyana haka da yake zantawa wakilimmu.

Ya ce, harajin zai tasiri sosai ga cigaba  na tattalin arziki  kuma duk wanda yake ganin sabanin hakan baiwa kasarnan adalci ba domin dama ana dogaro ne da man fetur da farashinsa ke cigaba da sauka  yanda ake saye da ba haka  yake yanzu ba kuma kudaden shiga da Gwamnati take dogara dashi kashi 90 daga mai yake.

Alhaji Mahmood  yace, a baya can harkokin noma sun taimaka wajen rike kasarnan  amma da aka sami mai sai aka watsar da dogara da noma. Amma ko a da dimma da ake noma ana biyan haraji ga kasa ana karbar haraji da jangali a wasu wurare harma duk mai gidan da yake da  samari majiya karfi a gida dole ya biya musu  haraji.

Ya yi nuni da cewa yanzu abubuwa sun dagulewa kasarnan tattalin arzikinta ya dogara da mai ne  komai ya yi baya yanzu ne Gwamnatin Buhari ke kokarin  farfado da noma da zai tallafawa cigaban arziki kuma ya zama wajibi a samo hanyoyi  na samun kudin shiga. A kasashen Duniya ba wata kasa da ba’a karbar haraji na “VAT”A nan kusa damu   kasar Nijar  da suke da karancin tattalin arziki ma suna biyan kashi 19 ne  kasar Kamaru na karbar kashi 18 haka ma kasar Ghana na karbar kashi 12.5 a kasarnan  a kashi 7.5  da ake karba yanzu ba karamin adalci aka yi ba ba zai yiwu ace ana hada-hadar  harkokin rayuwa  ace ba za’a biya haraji ba. Dole Gwamnati ta sami hanyoyin shigowar kudi  da za a sami yin ayyuka na cigaban kasa kamar titunan mota dana jirgi  makarantu da Asibitoci .

Shugaban Kamfanin na Miagro, Alhaji Mahmood Tauhid ya ce, a manyan kasashen Duniya Turai da Amurka yan kasa dole su biya haraji da ake gina cigaban kasa. Sannan karin  farashin kaya fiye da kima  da yan kasuwa suke a dalilin sanya harajin yakamata Gwamnati ta kafa wata hukuma mai karfin iko  da zai lura da farashi a hana tsuga farashi  domin bazai yiwu ana sai da  abu N500 ba ance zaka biya harajin kashi 7.5 sai ka maida kayan N1000  dama wasu  abinda sukeso kenan dasun sami dama sai su rika jingina dashi su cutar da jama’a.

Da wannan haraji Gwamnati za ta hana cigaban kasa  kuma a wannan Gwamnatin bisa jagorancin shugaba Buhari  ana samun cigaba ana abubuwa na cigaban kasa a fannoni da dama. Ita kuma Gwamnati  ta rika tabbatarwa  anyi amfani  da su yanda  yan kasa  zasu  amfana. Bambancin kasarnan da wasu kasashe shi ne in suka biya yan kasar za su amfana suna gani a kasa. Su kuma shugabanni  su tabbatar cewa  harajin ana aiki dashi yanda za su mora.

Tauhid ya ce, harajin ba karamin alheri bane ga kasa  suna fata dashi da wannan Gwamnati take na tabbatar da aiki da kudaden al’umma ya dore. Kuma duk wanda ya biya haraji yana da  damar  ya kalubalanci Gwamnati  akan abinda batayi maka ba.

Alhaji Mahmood Tauhid ya yi kira yan Nijeriya akan suyi biyayya ga Gwamnati wajen biyan haraji ita kuma dama Gwamnati tana bayyana  yanda  za ta kashe kudaden da  za ta samu  daga wasu bangarorin samun kudi har da na haraji, kuma su ‘yan majalisu  na tarayya dana jihohi aikin sune su rika bin diddigi  na yadda  ake  kashe kudi dan amfanin al’umma.

Exit mobile version