Connect with us

KASASHEN WAJE

Hizbolla A Brazil

Published

on

Jami’an yan sandan Brazil sun kama wani mutum dan kasar Labanon wanda Amurka ke zargin yana daya daga cikin manyan masu daukar nauyin kungiyar Hezbollah wato sojojin sakai na Lebanon.

An tsare Assad Ahmad Barakat a jiya Juma’a ne a birnin Foz do lguacu na Brazil, birnin da iyakokin kasashe uku na Brazil da Argentina da Paraguay suka hadu. Yankin dai dama ya yi kaurin suna a matsayin matattarar yan fasa kwauri, da masu buga jabun kayayyaki har ma da safara ba bisa kaida ba.

Jami’an yan sandan na Brazil sun ce “Yan kungiyar Barakat sun yi sayayyar kaya da kimar ta takai ta dalar Amurka miliyan 10, ba tare da bayyana kimar kayan ga gwamnati ba a wani gidan caca dake birnin Argentine na Iguazu da zummar boye kubaben kungiyar.

A cewar jami’an Argentina, kasar na zargin Barakkat da boye kudade a madadin kungiyar Hezbollah saboda haka ta kulle dukkanin kadarorinsa.

Ya zuwa yanzu ba a tabbatar da ko za’a yankewa Barakkat hukunci a Brazil ko kuma za a kai shi Paraguay ba.
Advertisement

labarai