Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce, ta ceto rayuka da dukiyoyi 26 da kudinsu ya kai Naira miliyan 17 daga gobara 22 da aka samu a watan Yuni.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Saminu Abdullahi, ya fitar ranar Talata a Kano.
- An Samu Gobara 258 Cikin Wata 3 A Jihar Kano
- Yadda Aka Yi Bikin Tunawa Da Ma’aikatan Kashe Gobara Na Duniya A Kano
Abdullahi ya bayyana cewa mutane tara ne suka mutu, yayin da gobarar ta lashe dukiyar da ta kai ta Naira miliyan 6.7.
“Hukumar ta amsa kiran ceto 18 da kararrawar kiran karya hudu daga mazauna jihar,” in ji shi.
Kakakin ya shawarci jama’a da su yi taka tsantsan wajen kashe gobara tare da ci gaba da share magudanar ruwa domin gujewa abubuwan da ba a zata ba.