Yayin da musulmai suka yi bikin Babbar Sallah, hukumar kula da ilimin Almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta, ta kara jaddada aniyarta ta daukar nauyin yara miliyan 10 da ba sa zuwa makaranta daga nan zuwa shekara ta 2027.
Babban Sakatare kuma Shugaban Hukumar; Dakta Muhammad Sani Idris, shi ne ya bayyana haka a sakonsa na barka da Sallah a ranar Lahadin da ta gabata, sannan ya jinjina wa kokarin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, na taimaka wa yara wadanda ba sa zuwa makaranta, inda ya kara jaddada mayar da hankali a kan lamarin ilimin yaran.
- Yadda Wike Ya Kafa Tirihin Gudanar Da Ayyukan Ci Gaba A Abuja
- Badaƙalar Bashin Kaduna: Abin Da Ya Sa Ba Mu Gayyaci el-Rufai Ba – Hon. Lawal
Kamar yadda ya ce, hukumar na matukar yin kokari yadda ya kamata; wajen kula tare da koyar da almajirai ilimi, inda ya kara jaddada aniyar tasu ta samar da tsarin ilimi mai nagarta, wanda zai bai wa yaran da ba sa zuwa makaranta damar samun kyakkyawar rayuwa a nan gaba.
Shugaban ya kara da cewa, “Ina isar da gaisuwata ga dukkanin al’ummar Nijeriya, wadanda suke yi mana fata na musamman; dangane da wannan daukar nauyi da wannan hukuma ke yi dangane abubuwan da suka shafi ilimin almajirai da yara kanana, wadanda ba sa zuwa makaranta.
“Ina yin kira ga masu ruwa da tsaki, da su kara mayar da hankali tare da himmatuwa a kan wannan lamari da ya shafi ilimi. Domin kuwa, ta hanyar ilimi ne kadai ake iya bai wa matasa dama, inda za su nuna kwazonsu domin a taimaka masu su kasance wadanda za su taimakawa al’umma a nan gaba.
“Ina mai nuna farincikina, a kan irin niyyar da Tinubu yake da ita na kawar da matsalolin da almajirai da yara kanana wadanda ba sa zuwa makaranta ke fuskanta a Nijeriya. Kulawar da yake nunawa a kan lamarin ilimi da ci gaban al’umma, hakan yana kara nuna wa ‘yan Nijeriya yadda gwamnatinsa ta mayar da hankali ga jin dadin ‘yan Nijeriya, musamman ma wadanda suke da bukatar a taimaka musu.
Bugu da kari ya ce, “Muna yin kokari wajen ganin sa lamarin ilimin Boko a cikin tsarin yadda za a koyar da wadannan almajira ,domin su ma su samu kyakkyawar rayuwa.
“Za kuma mu ci gaba da tuntuba da kuma yin hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki, wadanda suka hada da ma’aikatar ilimi ta tarayya da masu taimaka wa ci gaban ilimi, jihohi da kananan hukumomi, da su yi kokari wajen taimakawa dangane da matsalolin da suke addabar wadannan yara.
“Tsarin shugabanci na Shugaban Kasa Tinubu, na matukar taimakawa wajen cimma muradun; musamman ta yadda aka faro. Sannan, muna da tabbacin za mu tabbatar da sai kowane yaro ya kai ga samun hanyar samun ilimi mai nagarta ba tare da la’akari da yadda suka taso ko matsalolin da suke fuskanta ba”.