Daga Hussaini Baba, Gusau
Tsaftace muhalli shi ne ginshiƙin tsafta da kuma rigakafin kamuwa da ƙanana da manyan cututuka a tsakanin kowace al’umma.
Wannan ne ya sa Hukumar Tsafatace Muhali ta Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Mai baiwa Gwamnan Zamfara shawara a hukumar, Hon. Aliyu Ibrahim Magaji Ajala ya duƙufa ganin an tsaface faɗin jihar ta Zamfara.
Yanzu haka hukumar ta duƙufa wajen ganin ta kauda dukkan wata bola da yashe mugudanun ruwa a faɗin jihar. Har ila yau, hukumar ta samar da wadatatun kayan aikin tsaface muhali tun da ga cebura, baruka,da kwanoni ɗaukar shara.kuma motocin kwashe shara da katafiloli,tuni hukumar ta samar da su kuma ta inganta su ta yadda ba zasu bada matsala dan ganin an tsaftace jihar.
Shugabaun hukumar, Hon. Aliyu Ibrahim Ajala (Turakin Zurmi) ya bayayna cewa “Ƙudirin gwamnatin Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin mai daraja Gwamna Abdula’ziz Abubakar ne ya sa wannan hukumar babu dare babu rana ta duƙufa wajan ganin ta tsaftace jihar. Kuma hatta lokutan da ake ruwan sama ba dare ba rana wannan hukumar tsaye ta ke wajan yashe magudanan ruwa don kauce wa annoabar anbaliyar ruwa. Kuma wannnan shirin namu ya taimaka gaya wajan rashin samun ambaliyar ruwa a wannan shekara”.
Hon. Ajala ya kuma ƙara bayyana cewa “Hukumar na iyaka ƙoƙarinta wajan ganin ta magance duk abin da zai kawo ƙananan cututuka da manya da za su haifar da annoba a faɗin jihar ta Zamfara. Ƙofar wannnan hukumar a buɗe take wajan amsar ƙaugiyoyin aikin hanya daga unguwanin da garuwa dan haɗa ƙarfi wajan samar da tsaface muhali a faɗin jihar ta Zamfara. Kuma hukumar za ta yi iyaka ƙoƙarinta na ganin waɗanda su ka amsa kiran mu sun samu duk abunda su ke buƙata dan tsaftace muhali”, in ji shi.
Ya ƙara da cewa tuni wannann hukumar ta samar wa al’ummar jihar abubuwan zuba shara dan tara ta waje guda kuma lokaci bayan lokacin motocin da ta sayo za su bi suna kwashewa.
Hon Aliyu Ajala ya kuma nuna takaicin sa ga waɗanda ba sa amfani da robobin zuba shara a unguwanin, a maimakon haka sai su riƙa zubawa a kwalbatoci da kwatoci duk da kuwa akwai su a unguwani.
“Wannan cutar da kai ne da al’umma, dan haka na ke kira ga al’ummar wannnan jihar su taimaka wajen ba wa wannan hukumar haɗin kai dan ganin an samu ingantacciyar rayuwa da kuma bai wa gwamnatin Gwana Abdul’aziz Yari haɗin kai da adduo’i dan ganin ƙudirinta ya haƙƙaƙu na cigaban al’ummar wannan jihar da ƙasa baki ɗaya”, a ta bakinsa.