Abba Ibrahim Wada" />

Idan Za A Yi Adalci Barcelona Za A Ba Wa Laliga – Stoichkov

SOFIA, BULGARIA - MAY 19: Hristo Stoichkov, head coach of PFC Litex Lovech looks on during the Bulgarian A PFG League match between PFC CSKA Sofia and PFC Litex Lovech held on May 19, 2012 at the Bulgarian Army Stadium in Sofia, Bulgaria. (Photo by Nikolay Doychinov/EuroFootball/Getty Images)

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Hristo Stoichkob, ya bayyana cewa idan hukumomin kula da gasar laliga ta kasar Sipaniya za suyi adalci kungiyar Barcelona kawai ya kamata a bawa gasar laliga ta bana saboda Coronabirus

Kusan duk wani wasa a duniya ya sataya sakamakon annobar cutar Coronabirus sannan kasar Sipaniya itace kasa ta biyu a duniya da a yanzu cutar tafi yiwa illa inda mutane sama da dubu goma sha hudu suka rasa rayukansu sakamakon cutar.

Sai dai har yanzu babu tabbacin ranar da za’a iya komawa gasar ta bana saboda ba’asan lokacin da za’a iya shawo kan cutar ba amma tsohon dan wasan ya bayyana cewa idan har adalci za’ayi kowa ya tsaya a matsayinsa na yanzu wanda yake kafin a tafi hutun gasar hakan yana nufin Barcelona zata ci gaba da zama ta daya kenan.

“Bamason tsoro da abinda zia tayarwa da mutane hankali amma idan muka kalli yadda abubuwa suke tafiya tabbas akwai abin tsoro saboda haka kawai ayi adalci a bawa Barcelona kofi tunda sune na daya kowa sai ya zauna a matsayinsa” in ji Stoichkob

Barcelona dai itace a mataki na daya akan teburin gasar ta bana da tazarar maki biyu tsakaninta da Real Madrid wadda take mataki na biyu kafin a dakatar da wasannin laligar gaba daya saboda cutar.

Hukumar Laliga dai ta na fatan za a dawo, domin cigaba da buga wasannin na bana bayan da yanzu saura wasanni 10 a kammala kakar wasan ta bana kuma nan da watanni biyu ma za a iya dawowa idan an samu sauki.

Exit mobile version