Zaman lafiya shi ne ginshiKin duk wata rayuwa bama ace irin rayuwa ta iyali wadda idan aka yi sa a al’amura suna tafiya kamar yadda ya dace, shi kan shi ko su kansu masu irin wadannan halayen sai sun fi jin dadin rayuwar aure da matansu.
Awaiwani gidan da na sani ba fada mani aka yi ba,domin shi Maigidan abinda yake yi shi ne idan dan wancan matar ya isa ‘yaye sai ya kai ma kishiyarta ko abokiyar zama ta daya dakin.
Haka yake tafiyar da harkokin gidansa,wani yaron ma bai sanin mahaifiyarsa sai ranar daya kammala Jami’a, ko kammala yi ma Kasa hidima abinda aka fi sani da Bautar Kasa.Ita kuma ‘ya macen ba a nuna mata mahaifiyarta sai ranar da aka daura mata aure.
Yana kuma yin hakan ne domin ya samu hadin kan matan nasa wanda kuma haka abin ya kasance har bayan rayuwarsa.Zai kuma yi wuya ka shiga gida ka ji ana ta musanyar maganar da bata kamata ba tsakanin matansa.
Amma wasu Mazan ko Magidanta halayensu abin sai dai ayi sha’ani wai an cuci na Kauye, da zarar sun yi wani sabon aure sai su canza yadda suke tafiyar da al’amuransu.
Matarda Amarya ta tarar wato Uwargida sai a riKa ci mata mutunci ta hanyar yin abubuwan da basu kamata ba, Wata rashin jituwa ko tashe- tashen hankula tsakanin matansu, sune suke kasancewar mafarin faruwar al’amarin.
Daga Karshe dai wani har sai ya cimma burinsa na korar ita Uwargidan ta halayen shi daya canza, in aka samu wadda bata da haKuri koda kuwa ba sakinta yayi babata iya tsayawa da cigaba da ganin wulaKanci.
Baima tsayawa sai ta yi ma shi wani abinda bai dace ba tukuna hakanan sai ya dauki karan tsana ya riKa nuna ta da shi.