Yanzu haka, wasu kafofin yada labaru na kasashen yamma sun saba da yada labarin wai “Tattalin arzikin Sin na tafiyar hawainiya, abun da zai haifar da illa ga tattalin arzikin kasashen Afirka.” Ko haka batun ya ke?
A wajen wani taron manema labaru da wasu hukumomin Sin suka kira a birnin Beijing a yau, wani wakilin kamfanin Reuters mai dillancin labarai na kasar Birtaniya ya yi tambaya cewa, shin kasar Sin za ta iya cimma burinta na samun karuwar tattalin arziki da ta kai kimanin kashi 5% a bana? Daga baya, wani jami’i mai kula da tsare-tsaren tattalin arziki na kasar Sin ya amsa cewa, “Muna da sharadi, da kwarewar da ake bukata, gami da cikakken imani kan cewar za mu cimma burin da muka sanya a gaba, na raya tattalin arziki.”
- Fu Cong: Kasar Sin Tana Goyon Bayan MDD Don Kara Himma Da Inganci
- Sin Za Ta Dauki Jerin Matakai Don Ingiza Bunkasuwar Tattalin Arzikinta
To, me ya sa kasar Sin samun cikakken imani kan bunkasuwar tattalin arzikinta?
Dalili na farko shi ne, yanayi mai kyau na tattalin arzikinta cikin watannin da suka gabata. An ce, saurin karuwar tattalin arzikin kasar a watanni 6 na farko na bana ya kai kashi 5%, kana yanayin samar da guraben aikin yi, da na farashin kayayyaki, dukkansu na da karko.
Kana dalili na biyu, shi ne dimbin matakan da gwamnatin kasar ta dauka don sa kaimi ga karuwar tattalin arziki. Misali, samar da alfanu ga al’umma don habaka bukatun da ake samu cikin kasuwannin gidan kasar, da taimakawa kamfanonin da suka fada cikin mawuyacin hali, da neman farfado da kasuwar sayen gidaje, da inganta yanayin kasuwar hannayen jari, da dai sauransu. Bisa yadda aka samu dimbin zirga-zirgar masu yawon shakatawa a kasar Sin, da kyautatuwar yanayin kasuwar gidaje a Beijing da sauran birane daban daban, da hauhawar farashin hannayen jari, a kwanakin baya, za a iya ganin kyakkyawan tasirin matakan da aka dauka a kasar.
Sa’an nan ko imanin kasar Sin kan yanayin tattalin arzikinta zai yi wani tasiri kan kasashen Afirka, da sauran kasashe masu tasowa? A ganina, wannan imani zai haifar da kyakkyawan tasiri da hasashe mai yakini kan karuwar tattalin arzikin kasashe daban daban. Sa’an nan, za a iya tabbatar da gaskiyar maganar, ta hanyar duba wasu alkaluma masu alaka da kasar Sin:
A fannin samar da gudunmowa ga tattalin arzikin duniya, tun daga shekarar 1979 zuwa ta 2023, kasar Sin ta samar da gudunmowar kashi 24.8% na karuwar tattalin arzikin duniya, wadda ta kai matsayin koli a duniya.
Kana a fannin zuba jari ga kasashen waje, yawan jarin da kasar Sin ta zuba wa kasashen ketare da ba na fannin hada-hadar kudi ba, ya kai dalar Amurka biliyan 130.1, a shekarar 2023, jimillar da ta ninka ta shekarar 2003 sau 61, tare da kiyaye wata matsakaiciyar karuwa ta kashi 23% a duk shekara. Ban da haka, ya zuwa karshen shekarar 2023, adadin kudin da kasar Sin ta zuba wa kasashen Afirka kai tsaye ya zarce dalar Amurka biliyan 40. Ta haka, kasar ta zama daya daga cikin manyan kasashen da suka fi zuba jari a nahiyar Afirka.
Ban da haka, a fannin ba da tallafi ga sauran kasashe, tsakanin shekarar 2004 da ta 2009, yawan kudin da kasar Sin ta ba kasashe daban daban a matsayin tallafi ya kan karu da kashi 29.4% a duk shekara. Sa’an nan, daga shekarar 2013 zuwa ta 2018, yawan kudin da Sin ta ba sauran kasashe ya kai kimanin dalar Amurka biliyan 28.3, inda a cikinsu kudin da aka ba kasashen Afirka ya kai kashi 44.65%.
Wadannan alkaluma sun shaida cewa, “Idan kasar Sin ta samu ci gaba, to, duk kasashen duniya ma za su samu cikakkiyar damar raya kansu”. Kana wasu manufofi da kasar Sin ta gabatar, irinsu gina al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya, da gina “Ziri Daya da Hanya Daya”, da shawarar raya daukacin duniya, da dai sauransu, dukkansu sun nuna yadda Sin take nacewa kan more damar raya tattalin arziki tare da kasashe daban daban. Ta haka, maufofin kasar Sin sun samu amincewa da goyon baya daga dimbin kasashe, da kungiyoyin kasa da kasa.
Don tinkarar yanayin hawa da saukar tattalin arzikin duniya, dabarar da kasar Sin ta dauka ita ce, raya tattalin arzikinta, sannan daga baya ta sa kasashe daban daban samun ci gaba tare. Sabanin yadda wasu kasashen dake yammacin duniya suka saba yi, wato ta da rikici da lallata tattalin arzikin sauran kasashe, don neman samun karuwar tattalin arzikinsu. Wannan bambanci, babban dalili ne da ya sanya imanin Sin da hasashenta mai kyau ke ci gaba da haifar da tasiri mai yakini kan tattalin arzikin duniya. (Bello Wang)