Daga Abubakar Abba,
An tir da kisan kare dangi da ake yi wa wasu ‘yan Arewacin kasar mazauna kudu alhali ba su ji ba su kuma gani ba.
Shaharren masanin yanar gizo wanda kuma ke yin sana’ar kirkirar shafuka na yanar kizo Mal Aminu Iliyasu Kajuru ne yayi Allah wannan Allah wadan a hira da manema labarai a Kaduna.
A cewar Mal Aminu Iliyasu Kajuru, hakan ya nuna karara cewa kisan kare dangi da ake yi wasu ‘yan Arewan mazauna kudu.
Mal Aminu Iliyasu Kajuru ya ce, baya goyan bayan kisa ko wani iri ne ako wani yankin kasar na kuma a kan ko wacce irin alumma dake a fadin kasar nan.
A cewar Mal Aminu Iliyasu Kajuru, yana mamakin irin yadda Yarabawa masu daukan kansu a matsayin wadanda sukafi kowa ilimi a kasar nan, amma sai gashi sun tsunduma kansu cikin daukar doka a hannunsu da kuma hukunta wadanda ba su ji ba basu gani ba.
“Ina mamakin irin yadda Yarabawa masu daukan kansu a matsayin wadanda sukafi kowa ilimi a kasar nan, amma sai gashi sun tsunduma kansu cikin daukar doka a hannunsu da kuma hukunta wadanda ba su ji ba basu gani ba”.
Aminu Iliyasu ya kuma jinjina wa alummar dake a Areacin kasar nan, musamman matasa kan yadda suka nutsu ba su dauki doka a hannun sa ba a yayin da wasu ‘yan kabilyar ta Yarabawa suka yi wa wasu ‘yan Arewacin kasar kisan kare dangin.
A cewar Mal Aminu Iliyasu Kajuru, hakan ya nuna ‘yan Arewacin kasar nan, musamman matana dake a mazauna kudu masu bin doka da oda ne, inda ya yi kira a gare su ci gaba da nuna halin da’a da kuma dattako kamar yadda aka san yawancin ‘yan Arewa da irin wannna halin.
Ya kuma yi nuni da cewa, babu wani ci gaba da za a iya samar wa a cikin ko wacce alumma dole sai da zaman lafiya.
Mal Aminu Iliyasu Kajuru Kajuru yayi kira da shuwagabanni da su hanzarta daukan mataki kafin lokaci ya kure musu.