Abba Ibrahim Wada" />

Ina Son Ci Gaba Da Zama A Man. United Har Abada – DE GEA

Mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Dabid De Gea ya bayyana cewa yanason ci gaba da zama a kungiyarsa  har zuwa karshen rayuwarsa saboda kungiyar tayi masa duk abin da yake so a rayuwarsa.

Rahotanni daga kasar ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta kusa cimma yarjeejniya da mai tsaron ragar kungiyar, Dabid De Gea akan sabon kwantaragin da mai tsaron ragar zai kara,

Mai tsaron ragar yanason sake sabon kwantaragi a kungiyar kafin yatafi gasar cin kofin duniya da za’ayi a kasar Rasha wanda kuma zai zama dan wasa na biyu da zaifi daukar albashi a kungiyar bayan Aledis Sanches.

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dai itace take ta zawarcin mai tsaron ragar sai dai sabon kwantaragin da ake tunanin mai tsaron ragar zai kara zaisa dole ta hakura da neman mai tsaron ragar domin neman wani.

Ana tunanin dai Manchester United za ta kammala yarjejeniya da mai tsaron ragar a karshen wannan watan bayan da mai tsaron ragar ya buga wasanni 16 batare da an saka masa kwallo a raga ba.

Shima dan wasan an bayyana cewa yanason sake sabon kwantaragin ne kafin yatafi gasar cin kofin duniya saboda yanason zuwa gasar ta cin kofin duniya batare da ana maganar canja sheka ba zuwa wata kungiyar.

Mai tsaron ragar dai yabuga wasanni 232 a kungiyar kuma ya buga wasanni 91 batare da an saka masa kwallo a raga ba.

 

Exit mobile version