Dan wasan gaban tawagar Super Eagles ta Nijeriya, Alex Iwobi ya jefa kwallaye biyu a wasan da kungiyarsa ta Fulhma ta lallasa abokiyar karawarta Nottingham Forest da ci 5-0.
Iwobi ya fara jefa kwallo a minti na 30 da fara wasan kafin ya jefa ta biyu bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.
- Manchester City Tayi Rashin Nasara A Hannun Aston Villa Da Ci 1-0
- An Yanke Wa Wani Mutum Hukuncin Kisa A Zamfara Bisa Kashe Abokinsa Akan N100
Nasarar da Fulham ta samu akan Forest yasa ta koma matsayi na 12 akan teburin gasar Firimiya ta kasar Ingila.
Iwobi ya koma Fulham daga kungiyar kwallon kafa ta Everton a bana, inda zuwa yanzu ya jefa kwallaye 4 a wasanni 13 da ya buga mata.