Abdulazeez Kabir Muhammad" />

JAMB Za Ta Fitar Da Sakamakon Jarrabawa

Hukumar mai gudanar da jarabawar neman shiga jami’o’i (JAMB), ta ce a nan ba da dade wa ba za tura da sakonni ta wayar salula ga dalibai da suka rubuta jarabawa don sanar da su lokacin da za ta saki sakamakon jarabawar bana.

Rahotanni sun bayyana cewa hukumar JAMB ta ce nan da lokaci kadan za ta tura sakonni ga dalibai masu neman shiga jami’o’i domin sanar da su a kan lokacin da za ta saki sakamakon jarabawar bana da zarar ta kammala tantancewa.

Shugaban sadarwa na hukumar, Dakta Fabian Benjamin, ne ya sanar da hakan a cikin wata ganawa da ya yi da manema labarai a ranar Lahadi cikin birnin Legas. A cewar sa, Dakta Benjamin ya nemi dalibai da su kauracewa sauraron jita-jitar masu yada labaran kanzon kurege da rade-radin a kan sakamakon jarrabawar bana musamman a kafofin sada zumunta.

Rahotanni sun bayyana cewa, fiye da dalibai miliyan 1.8 masu neman shiga jami’o’i sun zana jarrabawar JAMB ta bana cikin dukkanin jihohi da ke fadin kasar nan daga ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu zuwa ranar Laraba, 18 ga watan Afrilun 2019. Hukumar JAMB bisa jagorancin Farfesa Ishaq Oloyede, ta yaba da salo, tsari da kuma yanayin da aka gudanar da jarrabawar bana. A cewar ta, jarrabawar bana ta tsarkaka daga magudi ko kuma kalubale sabanin yadda ta kasance a baya.

 

 

Exit mobile version