Jami’an tsaro a Jihar Katsina sun ceto mutane 10 da wasu ‘yan bindiga suka sace, tare da kashe ɗaya daga cikinsu yayin wani samame.
Waɗanda aka ceto sun haɗa da mata shida da maza huɗu, kuma an sace su ne a ƙauyukan Kiroro, Kabbi, da Dogon Marke a ƙaramar hukumar Musawa.
- Sin Ta Kara Wasu Kamfanonin Amurka 12 Cikin Jerin Wadanda Ta Dakatar Da Fitar Musu Da Wasu Kayayyaki Daga Kasar Sin
- Barcelona Ta Kama Hanyar Lashe Gasar Zakarun Turai A Karon Farko Bayan Shekaru 10
Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar Katsina, Nasir Mua’zu, ya ce an gudanar da aikin ceto ne da misalin ƙarfe 10 na dare a ranar 8 ga watan Afrilu a yankin Gidan Marke, bisa sahihan bayanan da jama’a suka bayar.
An gudanar da samamen ne ta haɗin gwiwar jami’an Katsina Community Watch Corps (C-Watch) da Rundunar ‘Yansanda.
“Dukkan mutanen da aka sace an ceto su lafiya kuma an mayar da su gida wajen iyalansu,” in ji Mua’zu.
Ya jinjina wa haɗin kai tsakanin jami’an tsaro da al’umma, yana mai cewa hakan ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar aikin.
Gwamnati ta yaba da ƙwazon jami’an da suka halarci aikin kuma ta sha alwashin ci gaba da yaƙi da ‘yan ta’adda a faɗin jihar.
“Za mu ci gaba da fatattakar waɗanda ke barazana ga zaman lafiya a Katsina. Za mu yi amfani da duk wata hanya da albarkatu domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a,” in ji Kwamishinan.
Ya kuma buƙaci jama’a su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai, yana mai jaddada cewa haɗin kan al’umma na da matuƙar muhimmanci wajen kawo ƙarshen ‘yan bindiga.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp