An ceto mutane 11 da ‘yan bindiga suka sace a ƙauyen Kaibaba, Gundumar Turba da ke ƙaramar hukumar Isa a Jihar Sakkwato.
Waɗanda aka ceto sun haɗa da mata bakwai, jarirai uku da matashi ɗaya.
- Majalisar Dattawa Ta Amince Tinubu Ya Sake Ciyo Bashin Dala Biliyan 21 Daga Ƙetare
- Sojoji Sun Kashe Kwamandan Boko Haram A Borno
Jami’an tsaro ne suka gano su a dajin da ke ƙaramar hukumar Zurmi a Jihar Zamfara.
Mataimakin Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Idris Mohammed Gobir, ya karɓi waɗanda aka ceto a gidan gwamnati, inda ya yaba wa jami’an tsaro bisa ƙoƙarinsu da jarumtarsu.
Ya ce gwamnatin Jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu ba za ta gaji wajen yaƙi da rashin tsaro a jihar ba.
Gobir ya bayyana cewa kowanne daga cikin waɗanda aka ceto zai samu Naira 100,000, buhun gero ɗaya da buhun masara ɗaya a matsayin tallafi.
Shi ma da yake magana, Shugaban ƙaramar hukumar Isa, Alhaji Sherifu Abubakar Kamarawa, ya gode wa gwamnatin jihar bisa taimakon da ta bayar, yana mai cewa hakan ya nuna damuwar gwamnati kan tsaron rayuka da jin daɗin al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp