Wasu ‘ya’yan jam’iyyar APC, a Jihar Kano sun bukaci shugabannin jam’iyyar da su gaggauta daukar tsauraran matakai kan mai taimaka wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, bisa zarginsa da rashin mutunta jam’iyyar na kin halartar taron kaddamar da yakin neman zabenta a jihar.
Mambobin sun zargi Bashir Ahmad da zabar wasan gasar cin kofin duniya da ake yi a kasar Qatar a daidai lokaci da jam’iyyar ke kokarin kaddamar da yakin zabenta a jihar.
Alhaji Samani Inuwa, daya daga cikin shugabannin jam’iyyar daga karamar hukumar Gaya, ya shaida wa manema labarai tare da wasu mambobin jam’iyyar cewa lamarin Ahmad ya wuce gona da iri.
Ya ce, “Ba mu fahimci yadda Bashir Ahmad ya zabi zuwa Qatar a lokacin da muke Kano muna karamar hukumar Gaya domin kaddamar da yakin neman zaben gwamna da sauran mukamai na jam’iyyar.
“Idan kowane dan jam’iyyar zai yi yadda Bashir ya yi, ba ma tunanin APC za ta kai ga lashe zabe, don haka ya kamata a gaggauta hukunta shi don ya zama darasi ga wasu.”
Haka zalika shugabannin jam’iyyar sun taya gwamna Abdullahi Ganduje murnar ganin an gudanar da yakin neman zaben gwamna a garin Gaya cikin kwanciyar hankali, inda suka tabbatar da cewa duk da rashin jituwar irin su Bashir Ahmad, APC ce za ta lashe zabe a Kano.
Bashir Ahmad, mai taimaka wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai ta yanar gizo, ya wallafa hotonsa a shafinsa na Twitter a wani filin wasa da ke Qatar yana kallonq wasan gasar cin kofin duniya.
Hoton ya janyo cece-kuce yayin da ‘yan jam’iyyar suka bayyana matakin da ya dauka a matsayin abin takaici.
Kokarin jin ta bakin Ahmad ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoto.