Connect with us

LABARAI

Jam’iyyar APC Ta Jinjina Wa Tsohuwar Minista Kan Ajiye Aiki Da Ta Yi

Published

on

Jam’iyyar APC ta bayyana murabus din da Ministan kudi, Kemi Adeosun ta yi da kuma karban murabus din na ta da Shugaba Buhari ya yi a matsayin abin yabawa da ke nu na gaskiyar wannan gwamnatin.

Mukaddashin sakataren yada labarai na Jam’iyyar, Yekini Nabena, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.

Adeosun ta tabbatar da rashin sahihancin takardar cire ta daga aikin masu yi wa kasa hidima a cikin takardan murabus din na ta, wanda kuma ta ce hakan zai iya shafan gaskiyan da ake kallon wannan gwamnatin tana da shi, in har ba ta ajiye aikin ba.

Da yake magana, Mista Nabena, ya ce gwamnatin ta APC ta bi diddikin wannan zargin da aka yi wa Ministan.

“Yanzun sakamakon binciken ya bayyana, an kuma yi abin da ya kamata a ce an yi, Ministan ta bi hanyar sauka ta hanyar girma da arziki.

Mista Nabena, ya taya Ministan murna kan saukan da ta yi, ya kuma yi mata fatan alheri a duk abin da ta sanya gaba.

Ya kara da cewa, gwamnatin Buhari, mai gaskiya ce a wajen gudanar da harkokin da suka shafi al’umma, don haka ba za a kyale duk wani jami’i da ke cikin gwamnatin da ya kasance da wani hali mara kyau ba.

Ya yi nu ni da cewa, abin da ya kara lalata gwamnatin PDP da ta gabata kenan, lalatattun jami’ai.

Ya ce, irin wadannan jami’an sukan ki amsa gayyatan majalisun kasa a lokuta masu yawa, sukan rufe tashoshin Jiragen sama saboda abokanan hamayyan su, sukan sayi motocin da harsashi ba ya huda su duk da dukiyar talakawa.

“Irin wadannan mugayen halayen na su ne suka sanya ‘yan Nijeriya suka zabi Shugaba Buhari a shekarar 2015, domin kawo karshen su,” in ji Mista Nabena.

 
Advertisement

labarai