Kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta Sin JKS da majalisar gudanarwa ta Sin sun fitar da “Ra’ayi kan bunkasa sabbin karfin samarwa mai dorewa”.
“Ra’ayin” ya gabatar da muhimman matakai 19 bisa la’akari da kirkire-kirkire a bangarori 5. Na farko dai, karfafa kirkire-kirkiren kimiya da fasaha. Inganta kirkire-kirkiren kimiya da fasaha na asali da masu kawo sauyi, hanzarta samun ci gaban muhimman fasahohin da ake bukata da kara karfin kasar a bangaren kimiya bisa manyan tsare-tsare, kuma da karfafa matsayin manyan kamfanoni ta fuskar kirkire-kirkiren kimiya da fasaha, da hanzarta juya sakamakon kimiya da fasaha zuwa karfin samarwa a zahiri.
Na biyu, ingiza hadin gwiwa mai zurfi tsakanin kirkire-kirkiren kimiya da fasaha da kirkire-kirkiren masana’antu. Gyara da bunkasa masana’antu na gargajiya, da bunkasa sabbin masana’antu, da tsara makomar masana’antu nan gaba, da ingiza hadin gwiwa mai zurfi tsakanin tattalin arziki mai samar da kayayyaki da tattalin arzikin yanar gizo, da aiwatar da shirin “AI +” a dukkan fannoni.
Na uku, mai da hankali kan ingiza kirkire-kirkire kan hanyoyi samun ci gaba. Gina tsarin tattalin arziki mai dorewa, kuma mai amfani da makamashi mai tsafta, ba tare da gurbata muhalli ba,sannan kuma a inganta manufofin ci gaba mai dorewa, da ingiza yi wa tsarin makamashi kwaskwarima.
Na hudu, ci gaba da ingiza kirkire-kirkire kan tsarin gudanarwa. Mai da hankali kan hadin gwiwa tsakanin kimiya da fasaha da tattalin arziki wajen zurfafa kwaskwarima a cikin gida, inganta tsarin kula da kasuwa, kara samar da sabbin kayayyakin hada-hadar kudi, da rarraba kayan samarwa na zamani a duk fadin duniya.
Na biyar, zurfafa kirkire-kirkire kan tsarin aikin ma’aikata. Horar da kwararru da ake bukata cikin gaggawa don bunkasa sabbin karfin samarwa, da inganta tsarin sauyawa ma’aikata wuraren aiki. (Amina Xu)














