Connect with us

RAHOTANNI

Jauharin Taron Ranar Marubuta Na Katsina:

Published

on

Manya Sun Gani Su Na Wasoso, Yara Sun Gani Su Na Alatsine!
Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya wanda aka gudanar daga ranar Juma’a 16 zuwa Lahadi 18 ga watan Maris a Jihar Katsina, karkashin jagorancin Malam Rabiu Na’auwa Balarabe bisa taimakawar wakilai na gamayyar kungiyoyin marubuta da wasu daga cikin manazarta adabi, kamfanoni da hukumomin gwamnati da kuma uwa uba gwamnatin jihar Katsina, wannan taro mai taken ‘Hoton Bahaushe A Cikin Rubutunsa’ ya ilimintar da marubuta da manazarta da masana al’ada da kuma masu sha’awar rubutu da su ka halarta ta yadda ba za a manta da shi ba a tarihin cigaban rubutaccen adabi. Manufar wannan take shi ne wannan taro ya duba yadda Bahaushe na wannan zamani ya ke wakiltar kansa a cikin rubuce-rubucensa na kaggagun labarai sannan kuma yadda ya kamata ya wakilci kansa a cikin rubutu.

•Sabuwar Fatawa Da Bukatar Fadada Bincike
Karkashin shugabancin Shehin Malami Prof. Ibrahim Malumfashi kwalliya ta biya kudin sabulu, don ya fitar da mabambantan kanu da za a gabatar a ranar taron. Sannan shehin Malamin ya nuna daga na gaba a ke ganin zurfin ruwa. Don haka ya gabatar da makala mai ratsa jiki da canza tunani wanda a ciki ya ke nuna cewar duk abinda marubuci zai rubuta kwaikwayon wani abu ne a rayuwar da ta ke gudana a kewayensa, ita ya ke rubutawa, ba wai kago wani abu ya ke yi ba, wanda da bai taba karo da shi ba a rayuwarsa ta zahiri, inda ya kawo misali da yadda a ka wassafa rayuwar mata masu zaman kansu a littafin ’Yartsana na Ibrahim Sheme. Wannan fatawa ta Farfesa Malumfashi ta jawo hankalin wasu masana; daga cikinsu akwai Shehin Malami Professor Abdulkadir Dangambo inda a ka bude wani sabon shafi na nazari bisa wannan ra’ayi na Farfesa Malumfashi. Daga karshe a ka cimma matsaya a kan za a fadada bincike wajen tabbatar da labaran nan kagaggu ne ko kuma kwaikwayo ne daga rayuwar zahiri.
Sauran malamai sun irinsu Farfesa Isah Mukhtar ya maimaita makalar da ya gabatar a taron farko da a ka yi a Kano, saboda muhimmancin makalar a wajen marubuta. Wannan makala ya yi ta ne a kan ‘Dabarun Rubuta Kagaggun Labarai’. Sannan Malam Sulaiman Mai-Bazazzagiya shi ma ya gabatar da tasa kan rubutattun wakoki. Shi ma Dr Adamu Malumfashi da ya yi tasa a kan rubutun wasan kwaikwayo (abinda ya ce a na yi ma sa rikon sakainar kashi ba a kulawa da shi, don haka ba su da abin da za su yi nazari a kai). A bisa wannan dalilin ne wasu daga cikin marubutan da su ke wajen su ka sha alwashin samar da irin wadannan littatafan, don cike gibin da ya ke mai tazarar gaske tsakaninsa da rubutun zube da na wasan kwaikwayo. Akwai kuma wadanda ba su samu damar zuwa ba, kamar su Farfesa Yusuf Muhammad Adamu, amma ya turo yaronsa, Muhammad Yusif Adamu, da takarda kuma an ba shi dama ya gabatar wa mahalarta taron.
Mahalarta taro sun yi tsokaci a kan wannan wakilci na Bahaushe a cikin rubutunsa. A bisa wannan lamari na wakilci ne shahararriyar marubuciya Fauziyya D. Sulaiman ta jawo hankali a kan a rage karyar arziki da abinda hankali ba zai iya dauka ba a cikin labarai, wanda shi ne babban abinda manazarta da ma makaranta ke yin kuka kansa.

•NNPC Da Samar Da Rahusa Ga Marubuta
Jami’an Northern Nigeria Publishing Company (NNPC) Zaria su ma sun halarci wannan muhimmin taro kuma sun bajekolin littattafansu, wanda yawa-yawan mahalarta taron ba su da su. Abin birgewa da dama daga littattafan marubutan da ke kiran kansu marubuta a yau an yi su ne tun kafin su zo duniya, amma har yau littattafan na nan iyalan marubutan na cin gajiyarsu maimakon nasu da a yau iyakarsu bakin Bata. Sannan sun kwadaitawa marubuta cewar har yanzu kofa a bude ta ke ga marubutan da su ke son dab’in littafi a wajensu za su samu rahusa, inda NNPC za ta bayar da rabin kudin bugu. Sun kuma wanke kansu zargin da a ke yi mu su na su ’yan gatan marubutan farko ne kawai, amma marubutan yanzu ’ya’yan bora ne a wajensu. Sun ce a’a a rashin kira ne karen bebe ya bata; duk wata dama da su Malam Abubakar Imam su ka samu, marubuta a yau za su same ta a NNPC.

•Dakin Karatu Kasa Da Muhimmancin Lambar Littafi (ISBN)
Jami’an hukumar kula da Dakin Karatu ta Kasa daga reshen jihar Katsina sun taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan marubuta a kan muhimmancin lambar ISBN, kasancewar da yawa yawan littafan kagaggun labarai na Hausa ba su da wannan lamba, don haka babu littattafansu a ma’ajiyar littatafai ta duniya (World Catalogue). An yi wannan tattaunawar a yammacin ranar taron tare da malaman jami’a da wakilan marubuta Littattafan Hausa da na shirin fim a tsarin ‘Round Table Discussion’ (Zauren Muhawara), inda daga baya sauran marubuta su ka tofa albarkacin bakinsu su ka fadi matsalolinsu, sannan su ka yi tambayoyi a kan yadda za su samu wannan lamba da kuma amfaninta.

•Kasagi da Wanzuwar Al’adar Turgeza
Umar Danjuma Katsina ya kawo CD na wakokin Turgeza na gada da a ke yi a zamanin da, inda ya yi hakan ne domin ya wanzar da al’adar ta yadda ba za ta bace ba kuma jama’a za su san al’adar har su koyi ko su yi amfana da darasi ko fasahar da ta ke cikin gadar. Ya kamanta wannan da yadda marubuta za su dage wajen yin bincike musamman a al’adunmu don musanya su da yadda marubuta a yau ke kwaikwayon Turawa da Indiyawa wanda wannan nakasu ne, don kuwa mu na da kyawawan al’adunmu birjik wadanda bincike ne zai gano su.

•Horas da Sababbin Marubuta
A rana ta uku, ranar karshe, an samu an horas da matasa masu sha’awar koyan rubutu, an horas da mutane kimanin 40 dabarun rubutu da sigar zama marubuci nagari abin alfaharin al’ummarsa.
Domin tabbatar da samun dorewar irin wadannan abubuwa na ilimi wannan taro ya ba wa yaran marubuta, wato matasa, damar su bajekolin abin da Allah ya hore musu na baiwa da ilimi, a ciki akwai yara irinsu Hasheem Abdullahi Tanko na Binyaminu Usman Polytechnic Hadejia da Ayuba Muhammad Danzaki da Adamu Tukur Miyetti. Dukkanin wadannan matasa sun bada tasu gudunmawa mai tsoka. Misalin irin wannan gudunmowar ita wacce Hashim ya kawo a makalarsa mai taken “Da Magani A Gonar Yaro”, inda ya jero abubuwa 17 da su ke samar da tauraro na barkwanci a rubutu. Makalar Farfesa Yusuf Adamu ta Zuwa Ga Matasan Marubuta ta zama fitila ga duk wanda ya shirya zai yi rubutu mai inganci.

•Ina Mafita?
Daga karshe kamar yadda ya zo a rahoton bayan taro da shugaban taro, Farfesa Malumfashi ya fada cewa sama da shekara 30 ya na halartar taron marubuta, amma bai taba zuwa wanda ya birge shi kamar na Katsina 2018 ba. Ya kamata marubuta su dabbaka kalubalen abubuwan da su ka karu da shi ya zamana an fara:-
1. Fara saka ISBN a littafi kuma a tabbatar ya shiga cikin ma’adani na duniya
2. Su tabbatar da sun mallaki wadannan makaloli domin inganta rubutunsu da mu’amalarsu ta yau da kullum.
3. Su yi kokarin samar da wasannin kwaikwayo, don manazarta da daliban adabi su amfana tunda su na kishirwar hakan.
4. A rinka samar da jigo mai kyau da amfani ga rayuwar jama’a, kamar yadda ya zo a makalar Farfesa Isa Mukhtar.
5. A rage kawo labaran da hankali ba zai dauka ba.
6. A wanzar da tsofaffin al’adu ta hanyar rubutu.
7. A samar da bincike kafin a yi kowane irin rubutu kamar yadda shawara ta zo a taron da ya wuce da wannan na yanzu.
Wadannan kalubale su ne abin da ya kamata marubuta su yi riko da su, domin samun cigabansu.
Alhamdulillahi an gama taro babu wata matsala da a ka fuskanta, sai ta rashin gudanar da daren marubuta, wanda marubutan su ka nuna bukatuwarsu a kan haka tunda sun yi guzurin labarai da za su gabatar a wajen duk da cewar rashin yin ba zai taba zama nakasu ba duba da irin abubuwan da a ka samar na karawa juna sani. Duk da wannan tsaiko an samu cewar sarakunan gargajiya, jami’an gwamnati, manazarta da mahalarta taro sun yaba da wannan taro da a ka gudanar a yini uku.
Bako na musamman, Alhaji Ibrahim Muhammad Danmadamin Birnin Magaji kuma kwamishinan kudi da kasafi na jihar Zamfara, ya yi rawar gani, domin an fara taro da shi an kammala da shi. Alhaji Salisu Dangulbi, shugaban karamar hukumar Maru da ke jihar Zamfara, shi ma ya yi rawar gani. Wakilin uban taro, Malam Ibrahim Ado Kurawa, ya sanya wa taron albarka.
Akwai shehunnan malamai da su ka zo su ka tallafi taron don ganin ya inganta. Akwai Farfesa Salisu Ahmad Yakasai da Farfesa Aliyu Bunza da Dr Ibrahim Satatima (shugaban sashen Hausa na Jami’ar Bayero) da Dr Dangulbi da Dr Umar Bunza da Dr Ahmad Bello.
Don haka abin da ya biyo bayan taro na korafin marubuta wannan ba ya cikin jauharin da a ke magana a kai na taro. Don haka mu ke fatan kada ya zama wani abu ne na nuna rashin godiya da siyasa da nuna kin cigaban jihar Katsina a sarari, amma shakka babu manya da masu ilimi da masu son cigaban marubuta da marubutan da ke fatan sauyi na alheri da wadanda su ka dauki nauyin taro, gwamnatin jihar Katsina, sun yi sambarka sun kuma yaba, illa wasu kalilan yara da su ka yi korafi. Don haka kwalliya ta biya kudin sabulu!!!
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: