Ma’aikatar tsaron kasar Sin ta ce jawabin jagoran yankin Taiwan Lai Ching-te, ya sake nunawa karara cewa shi mai haifar da matsala ne ga Taiwan, kuma barazana ga zaman lafiya.
Kakakin ma’aikatar Chen Xi ne ya bayyana haka yau Lahadi, lokacin da yake tsokaci kan jawabin da Lai Ching-te ya gabatar jiya Asabar, inda ya nanata ajandarsa ta ballewa, lamarin da ya haifar da zaman dar-dar a gabobi biyu na Zirin Taiwan.
A cewar kakakin, a shekarun baya bayan nan, hukumomin jam’iyyar DPP na Taiwan suna kokarin ingiza ballewa da watsi da batun dunkulewar kasar domin cimma muradun jam’iyyarsu da kawo tsaiko ga kwanciyar hankali a Zirin Taiwan da watsi da makomarsa.
Ya kara da cewa, rundunar sojin kasar Sin PLA, na gudanar da horo da atisaye kamar yadda ta saba a kusa da tsibirin domin dakile ayyukan masu neman ‘yancin Taiwan da ma masu tsoma baki daga waje, da kuma kare tsaro da lafiyar Sinawa na Taiwan. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)














