Jirgin kasa ya murkushe wani mawaki dan kasar Romaniya yayin da jirgin ya kashe shi yana watsa kansa kai tsaye a yanar gizo zuwa ga mabiyansa, yayin da ya kure karar waka yana sararo a cikin motarsa a garin Ploiesti da ke kasar Romaniya ta Prahova.
Hatsarin ya faru ga mai suna Tavy Pustiu dan shekaru 29 da haihuwa ne a lokacin da ya kure karar waka tare da matarsa a bayan motarsu, wanda hakan yasa basu ji tahowar jirgin ba, a yayin da jirgin kasan ya bugi motar ta vangaren fasinja.
A cikin faifan, ana iya ganin matar, ‘yar shekaru 24, tana doso wurin tsayawar mota na ketaren jirgin, amma ta kasa hango jirgin yana tahowa. Bayan ‘yan lokuta kadan, Mr Pustiu yafirgita yayin da ya lura
da jirgin yana doso motar tasu.
Hukumomi a gundumar Prahova sun tabbatar da mutuwar Mr Pustiu a cikin hatsarin yayin da matarsa wacce ba a bayyana sunanta ba, ke cikin mawuyacin hali a asibiti.
A cikin wata sanarwa, ‘yan sanda sun ce, “Sakamakon wani karo tsakanin jirgin kasa da mota a kan matakin tsallaka, wani matashi mai shekaru 29 wanda fasinja ne a gaban motar an bayyana cewa ya mutu kuma wata mace ‘yar shekara 24 da ke tuka motar ta samu munanan raunuka.
“Hatsarin ya faru ne saboda rashin bin ka’idoji a matakin wucewa. Jirgin kasan ya taso ne daga Maneciu da Ploiesti Sud gabanin afkuwar hatsarin, kuma hukumomi sun ce masu kashe gobara su sha matukar walaha wajen cire mutanen biyu daga jikin jirgin. Lamarin ya haifar da tsaiko na awanni da yawa a zirga-zirgar ababen hawa da na jirgin kasa.
A cikin abin da ya zama kamar wasa mai ban takaici saboda kaddara, kimanin wata daya kafin rasuwarsa, mawakin ya aika da sako ga Facebook yana cewa, “Wata rana, jirgin da bai dace ba zai kai ka inda ya dace.”