Rahotanni na cewa, a safiyar yau laraba ne wasu mahara da ba a san ko su waye ba suka afkawa ofishin hukumar masu yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) dake Wuse zone 7 Abuja.
Mai magana da yawon hukumar, Wilson Uwujaren, ya bayyana harin a matsayin wani harin ba zata.
Wilson ya kara da cewa, maharan sun afka ofishin ne dauke da muggan makamai da misalin karfe biyar na asuba, yayin da suka dinga bude wuta.
‘Sun farfasa wasu motoci da aka ajiye a harabar ofishin, amma daga bisani masu gadin wajen sun samu nasarar korar mutanen’, inji Wilson.
Rahoton yace, maharan sun tsere a motar su amma sun bar wasika, dake bayyana dalilin zuwansu ofishin, inda suka sanya sakon yin barazanar hallaka babban mai bincike a hukumar Ishaku Sharu.