Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Taraba, Hon. Kizito Bonzena, ya fice daga PDP tare da komawa APC, yana mai danganta wannan mataki da rikicin bangaranci da ke ci gaba da raba kawuna a PDP a matakin kasa.
Bonzena ya tabbatar da cewa wasu ƴan majalisa 15 ma sun miƙa takardun sauya sheƙa zuwa APC. Cikin su har da Mataimakin Kakakin Majalisa, Hamman Adama Abdullahi (Mazabar Bali 2); Jagoran Majalisa, Jethro Yakubu (Wukari 1); da Tafarki Eneme (Kurmi); da Akila Nuhu (Lau); da Musa Chul (Gassol 1); da Josiah Yaro (Wukari 2).
Sauran sun haɗa da Tanko Yusuf (Takum 1); da Veronica Alhassan (Bali 1);da Anas Shuaibu (Karim Lamido 2); da Nelson Len (Nguroje); da Umar Adamu (Jalingo 1); da Joseph Kassong (Yorro); John Lamba (Takum 2); da Happy Shonruba (Ardo-Kola); da Zakari Sanusi (Ibi).
- Rundunar Sojojin Sin Ta Yi Tsokaci Game Da Ratsawar Jiragen Ruwan Yakin Canada Da Australiya A Mashigin Tekun Taiwan
- Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan Ta’adda A Dajin Taraba
Kakakin ya bayyana cewa wannan mataki a lokaci guda ba wai don buƙatun kansu ba ne, sai don muradin ganin jihar ta ci gaba. Ya ce yanzu da dukkan ƴan majalisar 24 suka koma APC, majalisar za ta fi samun daidaito wajen aiki da manufofin gwamnatin jihar. “Jama’ar Taraba kada su yi kuskuren fassara wannan mataki. Don cigaban jiha muka yanke wannan shawara. Muna kuma roƙon mutane su ci gaba da goyon bayan gwamnati,” in ji shi.
Tsohon Kakakin Majalisar kuma ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Mbamnga, Peter Diah, ya tarɓi Bonzena da sauran waɗanda suka sauya sheƙa zuwa APC, yana mai cewa wannan babban sauyi ne a siyasar jihar.
Bonzena ya ƙara da cewa duk da cewa kafin yanzu APC ce ke da rashin rinjaye a majalisar, an ci gaba da aiki cikin zaman lafiya, amma yanzu yana farin cikin ganin cewa dukkan mambobin majalisar sun haɗe ƙarƙashin tsari daya da ya yi daidai da hangen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.













