Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Kalmar Shaidan

by
4 years ago
in WA'AZIN KIRISTA
3 min read
Wa’azin Kirista: An Siffanta Mutum Cikin Zunubi
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Wurin Karatu – Romawa 10:9,10,17

Kan Magana – Kalmar Shaidan

 

Labarai Masu Nasaba

MAHIMANCIN TAIMAKO 

Mahimmancin Taimako

“Gama idan ka shaida da bakinka Yesu Ubangiji ne, ka kuma bada gaskiya cikin zuciyarka Allah ya tashe shi daga matattu, za ka tsira: Gama da zu zuciya mutum yake bada gaskiya zuwa adilci; da baki kuma a ke shaida zuwa ceto. Bangaskiya fa daga wurin ji ne, ji kuma daga wurin maganar Kristi” (Romawa 10:9, 10,17)

Kalmar shahadan Kirista wata babban shaidan ce ta musamman ne da Kirista na shaidawa zuwa ga tabbacin imaninsa cikin Allah ubangiji makadaici. Kirista na kadaita Allah ubangiji bisa ga wannan ayar:

“Ka ji fa, ya Israila: Ubangiji Allahnmu Ubangiji Allahnka ubangiji daya ne: Kuma za ka kamnaci ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka da dukan karfinka” (Kubawar shari’a 6:4 – 5).

Wannan Kalmar shahadah tabbaci ne akan Allantakan Allah Ubangiji daya ne domin da haka duk mai imani da shi ya kamata a kadaitabhi a kuma bauta shi kadai domin baya tarraiya da kowa. Allah baya yi kama da kowa ba kuma har abada shine mai kowa da komai.

Matuka Kirista ya yi kalmar shahadah akan yesu Almasihu da kuma Allah ubangiji. To ya zama wajibi ne Kirista ya cigaba da kadaita Allah Ubangiji maitsarki Duk wanda ya kadita Allah Ubangiji to ya zama mashi doles ne ya bauta mishi cikin ruhu da gaskiya littafin yohanna 4:23 – 24).

Tushen kalmar shaidar Kirista na samuwa a wannan ayar watau littafin kubawar shari’a 6:4-5 sai kuma furucin tabbacin imanin Kirista na samuwa a littafin Romawa 10:9,10,17. A cikin addinin Kirista ko imanin Kirista, matuka Kirista ka imanin Kirista, matuka Kirista yayi imani da mutuwa yesu, Tashiwarsa daga matuttu, to zai tsira.

Cikon imanin Kirista a tattare da ba da gaskiya daga cikin zuciyarsa da cewa. Allah Ubangiji ya tashe shi daga matattu zai tsira. Bangaskiyar Kirista na faraway daga cikin zuciya ne da baki kuma ake shaidan bangaskiya zuwa ga ceto.

Bangaskiyar Kirista na tabbata ne akan mutuwar yesu Kristi akan giciye an kuma bizine shi, kuma yayi kwanaki uku a kabari kuma ubangiji Allah ya tashe shi daga matattu.

Bangaskiyar Kirista bai cika ba matuka Kirista bai da gaskiya da mutuwa da kuma tashiwan yesu Almasihu daga matattu.

Ga kowane Kirista kadaita Allah da imani ga abinda Allah ya fada ko ya saukar a cikin littafin maitsarki gama da yesu Almasihu shine imanin Kirista kuma a nan ne Kalmar shadan Kirista na samuwa. Imani Kirista da cewa Allah daya ne da kuma mutuwar yesu Almasihu domin ya cici duniya shine shaidan Bangaskiyar Kirista ko imani Kirista.

Wannan bangaskiyar Kirista daga zuciyarsa da kuma furuci daga bakinsa da ke kai Kirista ga tsira bat a yiwuwa sai tawurin ji bishara ko maganar Kristi. Watau babu wanda zai zama mai imani ba tare da baya ji Kalmar Allah ko maganar Allah ba ko kuwa Bisharar yesu Almasi hu ba. In kuma Kirista yana da imani akan yesu Almasihu to tabbaas ne Kirista ya yi shaidan imaninsa tawurin furucin imaninsa tawurin Kalmar Shahadah.

Bisharar ceto na samuwa ne tawurin maganar Allah da albishir da Allah ya bai wa duniya game da zuwan yesu Almasihu domin ya cici duniya daga zunubi.

Allah ya tabbatar mana a cikin littafin maitsarki da cewa yesu Almasihu kalmarsa ne, Rahamarsa ne, Jinkan ne, shine maiceton duniya matuka an bada gaskiya a gareshi. Wannan bangaskiya a gareshi. Wannan, bangaskiya ga yesu Almasihu ba zai taba cikin ba sai Kirista ya yi imani da dalilin da Allah ya aiko shi a duniya da cukka ayukan da yayi watau wahadan day a sha domin gafara zunubanmu. Watau a takaice, zuwan yesu Almasihu da ayukansa, wahalar da yasha domin ceton bil Adama da kuma tabbacin tashiwarsa akan matatau duka sune cikon nasin ubangiji Allah.

Littafin maitsarki ya tabbatar mana da cewa yesu Almasihu ayar Allah ne. To da sunayensa masu girma sun kara tabbatar mana da matsayin yesu Almasihu gaban Allah, shi yasa imanin Kirista na da tushe ko kuma ya ginu ne akan matsayin yesu Almasihu ne ya tabbatar mana da cewa imanin Kirista shine yesu Almasihu ya mutu kuma Allah ubangiji Allah ya tashe shi daga matatu shine tsian kowane irin matum da ya bada gaskiya ga wannan bishara. Matuka Kirista yana da wannan imani, to lallai ne ya tabbatar da wannan imanin yawurin furuta da bakinsa kuma daga cikin birnin zuciyarsa to ta haka ne Kirista zai sami tsira ko ceton Allah.

Atakaice shine Allah daya ne ko kuwa kadaitan Allah, da imani cewa yesu Almasihu ya mutu kuma ya tashi daga matatu watau Allah ya tashe shie a kwane na uku. To wannan tabbacin ceton mai furucin kenan.

Domin da hak duk wanda – ya bada gaskiya da cewa yesu ya mutu Allah ya tashe shi daga matattu, wannan shahadah.

ADVERTISEMENT

Allah ya tabbatar mana da imanin mu ya kuma tabbatar wa wasu imaninsu zuwa ga tsira.

Shalom! Shalom!! Shalom!!!

 

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

A Na Zargin Shugaban APC Da Sama Da Fadin Naira Miliyan Bakwai A Kebbi

Next Post

Ka San Jikinka: Jikinka Duniyarka

Labarai Masu Nasaba

Taimako

MAHIMANCIN TAIMAKO 

by
10 months ago
0

...

Rashida Mai Sa’a

Mahimmancin Taimako

by
11 months ago
0

...

Adalci

A Kawar Da Kwadayi Domin A Yi Adalci

by
12 months ago
0

...

Mahimancin Taimako

Mahimancin Taimako

by
12 months ago
0

...

Next Post

Ka San Jikinka: Jikinka Duniyarka

Leave Comment

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: