Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa (NiMet) ta yi hasashen samun ɗan hazo mai ɗauke da ƙura a wasu sassan jihohin Jigawa, da Kano, Katsina, da Kaduna, da Zamfara, da Kebbi da Sokoto a ranar Litinin, 26 ga Oktoba, 2026.
A hasashen yanayin da hukumar ta fitar, ta ce ana sa ran samun yanayin rana a yankin Arewa maso Gabas a tsawon lokacin hasashen. A yankin Arewa ta Tsakiya kuwa, ana sa ran samun sararin sama mai rana tare da wasu gajimare.
NiMet ta kuma yi hasashen yiwuwar tsawa da ruwan sama mai kaɗan a wasu sassan jihohin Kogi, daga Kwara, da Binuwai, da Nassarawa da Babban Birnin Tarayya, Abuja.
A yankin Kudancin Nijeriya, hukumar ta ce ana sa ran samun gajimare tare da ɗan hasken rana da yiwuwar tsawa da ruwan sama kaɗan a wasu yankunan bakin teku. Daga baya da rana zuwa yamma, ana sa ran tsawa da ruwan sama a wasu jihohin yankin.
Hukumar ta shawarci jama’a, musamman masu fama da asma da sauran matsalolin numfashi, da su yi taka-tsantsan a wuraren da ƙurar hazo za ta shafa, domin ƙurar na iya rage ingancin iska da kuma ganin hanya. Ta kuma bukaci masu ababen hawa su yi tuƙi cikin kulawa idan gani ya ragu.














