Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Farfesa Isa Ali Pantami, ya ce nan ba da jimawa ba zai bayyana sunayen mutanen da yake zargi da ƙoƙarin kawo cikas ga burinsa na tsayawa takarar gwamnan Jihar Gombe a zaɓen 2027. Pantami ya buƙaci magoya bayansa da su ci gaba da addu’o’i, kada su bari sukar da ake yi musu ta raunana musu gwiwa.
Pantami ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Asabar. Ya gode wa al’ummar Gombe da suka ci gaba da yi masa addu’o’i a masallatai da majami’u, tare da karatun Alƙur’ani da sauran ibadu domin neman nasarar tafiyarsa ta siyasa. Ya ce goyon bayan da suka nuna masa ya ƙara masa ƙwarin gwiwa da jin cewa yana da mutanen da ke ƙaunarsa.
Ya kuma buƙaci magoya bayansa da kada su fusata ko su karaya saboda sukar da ake musu, musamman kan yadda suke neman taimakon Allah ta hanyar addu’a. A cewarsa, bai kamata su bari abin da wasu ke faɗa ya hana su ci gaba da ayyukansu na alheri ba.
Pantami ya yi zargin cewa binciken da tawagarsa ta gudanar ya tabbatar da cewa akwai mutanen da ke kashe kuɗi da ƙoƙari domin daƙile tafiyarsa ta siyasa. Sai dai bai bayyana sunayen waɗanda yake zargi ko kuma hujjojin da binciken ya gano ba. Ya ce zai bayyana cikakkun bayanai kan zargin da kuma mutanen da yake ganin suna da hannu a ciki nan ba da jimawa ba.
Burinsa na zama gwamnan Gombe ya fuskanci ƙalubale bayan ya fice daga jam’iyyar APC ya koma PDP, inda ya zama ɗan takarar gwamnan jam’iyyar a zaɓen 2027. Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta cire sunansa daga jerin sunayen ƴan takarar da ta fitar a watan Oktoba, lamarin da ya haifar da rashin tabbas kan ko zai iya shiga zaɓen.
Duk da haka, Pantami ya bayyana cewa matsalar ƙalubale ce ta wucin gadi, yana mai cewa zai ci gaba da fafutukar tabbatar da burinsa.














