Rundunar Ƴansandan Jihar Bauchi ta kama wata mata mai shekaru 18, mai suna Fatima Dalha, bisa zargin caka wa mijinta mai shekaru 30 wuƙa a ciki yayin wata taƙaddama ta cikin gida a Ƙaramar Hukumar Dass ta jihar. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:00 na safiyar Lahadi, 25 ga Oktoba, 2026, a yankin Lirr Bajar.
Rahotanni sun bayyana cewa rigimar ta samo asali ne daga saɓani kan kuɗi, da kayan sawa da kuma wayar salula da matar ta ce mallakinta ne. An ce taƙaddamar ta tsananta har ta rikiɗe zuwa faɗa, inda ake zargin matar ta ɗauki wuƙa ta caka wa mijinta a ciki.
Jami’an ƴansanda daga ofishin Dass sun isa wurin bayan samun labarin lamarin, inda suka kai mutumin asibiti domin samun kulawar likitoci. A halin yanzu, yana karɓar magani. Kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP Nafiu Habib, ya ce jami’an sun kuma kuɓutar da matar daga hannun fusatattun mutane da suka yi ƙoƙarin yi mata hukuncin kisa ba tare da bin doka ba.
Rundunar ta tabbatar da cewa an tsare wadda ake zargi, tare da ƙwace wuƙar da ake zargin an yi amfani da ita wajen kai harin. Ana sa ran miƙa lamarin ga sashin binciken manyan laifuka na jihar domin gudanar da cikakken bincike.
Kwamishinan Ƴansndan Jihar Bauchi, Sani-Omolori Aliyu, ya nuna damuwa kan yawaitar rikicin cikin gida tsakanin matasan ma’aurata.
Ya shawarci ma’aurata da su riƙa warware saɓani cikin lumana ta hanyar neman shawarar dangi, da dattawan ko bin hanyoyin da doka ta tanada, maimakon amfani da tashin hankali. Ya kuma gargaɗi jama’a kan ɗaukar doka a hannunsu, yana mai cewa ya kamata a bar jami’an tsaro su gudanar da bincike bisa ƙa’ida.













