Adadin mutanen da suka mutu sakamakon harin ƴan bindiga a jihar Taraba ya ƙaru zuwa aƙalla 50, bayan an gano wasu gawarwaki a wani kogi. Rahoton Vanguard na ranar Litinin, 26 ga Oktoba, 2026, ya ce mazauna yankin da ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International ne suka tabbatar da ƙarin adadin ga kamfanin dillancin labarai na AFP.
Maharan, waɗanda ake zargin ƴan bindiga ne, sun shiga garin Binnari da ke gabashin jihar Taraba a ranar Juma’a, jim kaɗan bayan sallar Juma’a. Sun kashe mutane da dama, tare da ƙona shaguna da kuma kwashe kayayyaki daga wasu wuraren kasuwanci.
Wani mazaunin yankin, Bashir Mamuda Musa, ya ce an gano gawarwaki bakwai a ranar Juma’a bayan harin. A ranar Asabar kuma, an gano wasu gawarwaki 43 a cikin kogi, lamarin da ya kai adadin waɗanda aka gano sun mutu zuwa 50. Wani mazaunin yankin, Abdullahi Zakari, shi ma ya tabbatar da wannan adadi.
Rahotanni sun nuna cewa wasu mazauna garin, ciki har da mata da yara, sun gudu zuwa kogin domin tsira daga maharan, amma da dama sun nutse. Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, Victor Msheliza, ya ce jami’an tsaro na ci gaba da bincike a yankin tare da neman wasu gawarwaki.
Sai dai Amnesty International ta bayar da adadin mutanen da suka mutu har 52, tana mai cewa maharan sun kora wasu daga cikin mutanen zuwa cikin kogin yayin da suke ƙoƙarin tserewa.
Ƙungiyar ta kuma zargi hukumomin Nijeriya da gazawa wajen kare al’ummomin karkara da kuma hukunta waɗanda ake zargi da aikata irin waɗannan hare-hare.














