Hukumar Zaɓe ta Jihar Kano (KANSIEC), ta ayyana kudin miliyan 10 a matsayin kudin fom din ‘yan takarar shugabancin ƙananan hukumomi a zaben da za a gudanar nan gaba.
Masu takarar Kansila kuwa za su biya Naira miliyan biyar domin sayan fom din takararsu.
- WATA SABUWA: Ganduje Ya Nuna Rashin Jin Daɗi Bayan Tinubu Ya Masa Tayin Muƙamin Jakada
- Shekaru 60: DICON Ta Taimaka Wajen Samar Mana Da Makamai – Janar Musa
Shugaban hukumar, Farfesa Sani Lawan Malumfashi ne, ya bayyana hakan yayin gabatar da jadawalin lokacin zaben kananan hukumomin jihar ga wakilan jam’iyyun siyasa.
Ya kuma bayyana cewa dole ne masu takarar shugaban karamar hukuma su kasance sun kai shekaru 30 da haihuwa, yayin da masu takarar Kansila su kasance suna da shekaru 25 zuwa sama.
Za a fara yakin neman zabe a ranar 6 ga watan Satumba, 2024, sannan za a kammala a ranar 31 ga watan Oktoba, 2024.
Farfesa Malumfashi, ya jaddada cewa hukumar za ta hukunta duk wanda aka samu da laifin almundahana ko cin hanci.
Ya kuma gargadi jam’iyyun siyasa da su tabbatar sun gudanar da tarukan yakin neman zabe cikin lumana.
Kazalika, ya jadadda cewar hukumar za ta gudanar da zabe na gaskiya da adalci.