Connect with us

CIWON 'YA MACE

Kar Ki Yarda Miji Ya Fifita Soyayyarki A Kan Mahaifiyarsa

Published

on

Na dauko wannan batun ne a wannan makon sabo da duba da yadda matan wannan zamanin su ka dauki uwar miji a matsayin matsala a rayuwar aurensu, haka uwar miji ta dauki matar danta matsala a gare ta wanda abin ba haka ba ne. Ba zan ce ga in da matsalar ta ke kai tsaye ba sai dai zan iya dora laifin ga dukkan bangarorin biyu wato bangaren mata, uwar miji, ‘yan uwan miji da maigida.

Mata: Na fara daukar bangaren mata ne saboda a akan su na ke magana don yadda mata da yawa ke zaman tsama ko gaba da uwar miji wanda hakan ba daidai ba ne. Duk wacce ta haifa miki miji abokin rayuwa ta wuce wulakanci ko tozarci a gare ki, girmamawa da mutuntawa kawai zai ci gaba da wanzuwa a tsakaninku,ta yaya ki ke ganin maigida zai so ki kuma ya kaunace ki alhali baki dauki mahaifiyar sa a bakin komai ba? Ko bai fada ba zuciyar sa ba ya na jin ba dadi.
Uwar Miji: Iyayen miji musamman mata kan tsangwami sirakanansu da saka mu su karan tsana na ba gaira ba dalili, watakila su na tunanin maigida ya fi son matar a kan su ko ya na mata wani abu da baya musu wanda ba haka ba ne, idan mace ta zabi danki a matsayin wanda za ta rayu da shi har karshen rayuwarta to kuwa kamata yayi ki kyautata mata iyakar iyawar ki a matsayinki na wacce aka zabi wanda kika haifa cikin sauran mazan duniya.
‘Yan’wan Miji: Mafi aksari ‘yan uwan miji ke kara hura wutar husuma da ke faruwa tsakanin uwar miji da sirikarta, musamman in ba gida daya su ke ba ko gari daya, sai ya zamto duk abinda su ka gani a can za su kara a lokacin da su ka zo ba wa mahaifiyar su labari, wanda yin hakan ba abu ne me kyau ba.
Maigida: Shi maigida (miji) kamata yayi ya zama tsayayye kuma jajirtacce a cikin gidan sa ta yadda zai bawa kowa hakkinsa ba tare da ya shiga hakkin dayan ba. A Lokuta da dama magidanta kan gaza, ta wannnan bangaren ta yadda su na kallo mata na cin mutuncin mahaifiyarsu su kasa daukar mataki, ko su na ganin uwar miji da ‘yan uwan miji su tsangawami mata amma ya kasa daukar mataki har sai abu ya baci.
Matsalolin da Irin Wannan Zama Ke Haifawa:
Akwai matsaloli masu tarin yawa a kasan wannan rubutu, kadan daga cikinsu su ne:
1:Ya na haifar da raini a tsakanin uwar miji da sirikarta.
2:Ya na haddasa gaba a tsakanin uwar miji da sirikarta.
3:Ya na jawo tsana ga yaran da matar za ta haifa ga uwar miji da danginta, su ji ba sa son yaran.
4:Ya na haifar da yawan fada a wannan gida tsakanin mata da dangin miji.
5:Ya na nesanta mutum da Allah ta yadda dukkanin bangarorin za su fantsama neman sihiri wurin gabin sun mallaki maigida.
6:Yawan sihirce-sihirce zai gigita maigida har ya rasa nitsuwarsa.
7:Ya na haifar da rashin kwanciyar hankali wa dukkan bangarorin.
8:Ya na jawo mutuwar aure ta yadda uwa za ta tirsasa danta sai ya saki matarsa har ta yi ikrarin in bai saka ba za ta yi masa baki.
9:Har kisa ya na haifarwa.
Da sauransu.
Mata ina mafita?
Mafita a nan su ne:
1:Dukkanin bangarorin su ji tsoron Allah su tsarkake zukatansu su yi zama domin Allah.
2:Mata idan sun dauka cewar dukkanin rayuwar aure ibada ce to su dauki duk wani kalubale da zasu fuskanta dangane da uwar mici wani mataki ne na son cinye jarabawar da Allah ya basu kar su dauke ta a matsayin matsalar hana su yin abin da ya dace.
3:mata kar su tauye wa uwar miji hakkin nta da ya rataya akan danta, kuma kar su hana shi kyautata mata.
4:Mata kar ku zama masu kai korafin ‘yan uwan miji da mahaifiyarsa wurin maigida.
5:Iyaye mata (uwar miji) kar ku kalli sirakananku a matsayin matsalar ku.
6:ku daukesu tamkar ku, ku ka haife su.
7:karku yadda sauran yaranku su yi ta haddasa fitina a tsakaninku.
8:Yan uwan miji kowa ya tsaya a matsayinsa.
9:maigida ya zama ya na sa ido sosai ganin wata matsala ba ta faru ba a tsakanin mahaifiyarsa,matarsa,da kuma ‘yan uwansa ba. Kowa ya tsaya a matsayinsa da kuma ganin ya aiwatar da bangarensa na kasancewa a wannan matsayi.
10:sannan maigida ya zama wanda baya karbar zuga daga ‘yan uwansa don ya muzguna wa matar sa,sannan kar ya karbi zugar matarsa don ya muzgunawa ‘yan uwansa.
Shawara ga mata
Shawarata a nan ita ce karki yarda maigida ya fifita soyyayar ki fiye da ta mahaifiyarsa domin wannan ne mafarin rigimar. Ki dauki uwar miji tamkar mahaifiyar ki,ba ina nufin ki dai-dai-ta soyyayar ba kamar yarda za ki so mahaifiyarki ba a’a, ki girmama ta, darajata tamkar yadda ki ke wa mahafiyarki domin yadda kika mata haka wata rana ke ma za a miki a lokacin da ki ka zama uwar miji. ‘yan uwan miji su daina shiga harkar gidan dan uwansu har ya haifar da matsala. Uwar miji ta zama me kawar da kai, hakuri da hangen nesa ta yadda mutuntawa ne kawai zai faru a tsakanin ta da sirikarta domin abin da ta yi wa ‘yar wani haka zaa yi wa na ta yaran. Maigida ya zama me kyautatawa da biyyaya ga mahaifiyarsa, kyautatawa da adalci ga matarsa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: