Ba tare da shakku ba, Nijeriya na daga cikin manyan kasashen Afirka da ke kan gaba a tsarin fintech, wanda ke samun goyon baya daga ingantaccen tsarin manufofi, sauye-sauyen dokoki, da kuma ingantacciyar cibiyar biyan kudi ta dijital. Wannan ci gaba ya samar da yawaitar sabbin kirkire-kirkire da ke jan hankalin masu amfani da shi, sakamakon tasirin da yake da shi a fannonin tattalin arziki daban-daban.
Domin kara karfafa wannan matsayi, dabarar Babban Bankin Nijeriya (CBN) an tsara ta ne a tsanaki da nufin sanya wadannan tsarukan ba kawai su kasance jagorori wajen amfani da fintech ba, har ma su zama masu bayar da gudummawa wajen tsara hanyoyin dokoki, tsarin kirkire-kirkire, da ginshikan amincewa da suka dace da kasuwanni masu tasowa da kuma wadanda ke da saurin bunkasa a duniya.
- Sin Da Amurka Na Ci Gaba Da Musayar Bayanan Sirri Kan Yaki Da Miyagun Kwayoyi
- Manoma Da Makiyaya Sun Kulla Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Filato
A kan wannan tafarki, babban bankin ya samar da wani rahoto ta hanyar fadada tuntuba da masu ruwa da tsaki, tare da samun goyon bayan wani bincike da aka gudanar a cikin tsarin fintech. Rahoton ya tantance halin da tsarin fintech a Nijeriya ke ciki a halin yanzu, ya gano muhimman abubuwan da suka kamata a ba fifiko, sannan ya fayyace hanyoyin manufofi da za su jagoranci mataki na gaba na ci gaban wannan tsari.
Rahoton ya nuna wata muhimmiyar dama ga Nijeriya na jagoranci ba wai kawai wajen karba da amfani da fintech ba, har ma wajen tsara makomar fintech a matakin duniya, muddin ta kara karfafa hadin gwiwa tsakanin masu tsara dokoki da masu kirkire-kirkire, ta inganta cibiyoyin more rayuwa da sauye-sauyen manufofi, sannan ta bayyana ci gaban da ake samu cikin bayyananniyar hanya.
Rahoton ya kuma yi la’akari da girman yawan mu’amalar biyan kudi a Nijeriya, girman tsarin biyan kudi na kai-tsaye, da kuma kwarewar kasar wajen sarrafa sabbin kirkire-kirkire a tsakanin jama’a masu yawa. Haka zalika, Nijeriya na kara zama kasa da ba wai kawai kasuwa ce mai saurin bunkasar fintech ba, har ma abin koyi da darussan dokokinta ke da muhimmanci ga sauran kasashe masu tasowa da kuma tattalin arziki masu saurin bunkasa a duniya.
Bayanan da suka fito daga tattaunawar Babban Bankin Nijeriya (CBN) da masu ruwa da tsaki a tsarin fintech sun karfafa wasu muhimman abubuwan da ya kamata a ba fifiko a mataki na gaba na bunkasar wannan tsari. Daga cikinsu akwai karuwa da sha’awa kan tsarin kadarorin dijital na kasa, wanda aka tattauna a matakin misali da bincike kawai, a matsayin wani bangare na tattaunawa mafi fadi kan rage asarar kudaden waje da kuma karfafa hanyoyin tura kudi ta hanyar da ta dace da ka’idoji.
Abin lura ne cewa Nijeriya ta dade tana kan gaba wajen kirkire-kirkiren kudaden dijital. Tun a shekarar 2011, kasar ta aiwatar da tsarin biyan kudi na kasa baki daya mai aiki kai-tsaye da kuma hadin gwiwa tsakanin bankuna, wanda ya sanya tura kudi nan take tsakanin bankuna wanda ya zama ruwan dare a rayuwar kudi, tun kafin hakan ya zama gama gari a yawancin kasashe masu ci gaba da ma wadanda ke tasowa.
Rahoton ya bayyana cewa an ci gaba da wannan kwarewa tare da kara zurfafa ta ne ta hanyar kyakkyawan hadin gwiwa tsakanin Babban Bankin Nijeriya (CBN) da NIBSS, da kuma sauran masu ruwa da tsaki a tsarin biyan kudi. Wannan hadin gwiwar ta sanya tsarin biyan kudi nan take na Nijeriya ya zama daya daga cikin mafi girma, mafi juriya, kuma mafi yawan amfani da tsarukan biyan kudi na kai-tsaye a duniya.
A cewar rahoton, fiye da kashi 25 cikin 100 na dukkan mu’amalolin kudi ta na’ura a Nijeriya ana sarrafa su ne ta hanyoyin biyan kudi na kai-tsaye, ta hanyar dandalin NIBSS NIP.
A wannan fanni, an sarrafa kusan ma’amaloli biliyan 11 a shekarar 2024, daga biliyan biyar a shekarar 2022, lamarin da ya sanya Nijeriya cikin kasashen da suka fi karba da amfani da wannan tsari a duniya, tare da zama jagora a fili a nahiyar Afirka.
Wannan ya yi daidai da Hangen Tsarin Biyan Kudi na 2025 wato (Payments System Bision 2025), wanda ya sanya cimma yadzuwar biyan kudi ta lantarki (e-payment) zuwa shekarar 2030.
Rahoton ya nuna cewa duk da manyan nasarorin da aka samu a wannan bangare, kasar na ci gaba da fuskantar wani na’in suna mara kyau da ke da alaka da damfarar kudi ta dijital. A ra’ayin marubuta rahoton, damfara na ci gaba da zama babbar kalubale mai canzawa, wanda ke haifarwa daga hadin gwiwar laifuffukan cikin gida da kuma na ketare da ke amfani da dandamalin dijital na duniya.
Rahoton CBN ya lura cewa yayin da wasu dabarun damfara ake aikata su ne a cikin gida, hadin gwiwar jami’an tsaro da kuma shari’o’in da aka yi kwanan nan sun nuna cewa wani kaso mai yawa na laifukan kudi ta dijital da ake dangantawa da Nijeriya ana shirya su ne daga kasashen waje ko ta hanyar masu aikata laifi na ketare iyaka, inda galibi ake amfani da Nijeriya a matsayin tushe ko wakili, ba wai a matsayin ainihin tushen laifin ba.
Duk da haka, masana na bayyana cewa Nijeriya na samun ci gaba mai gamsarwa kuma a bayyane wajen tabbatar da ingancin tsarin kudi. Misali, karfafa kulawa kan yaki da halatta hanyoyi samun haramtattun kudade (AML), tsauraran ka’idojin sanin abokin hulda (KYC), da kuma karararn matakan aiwatar da doka sun taimaka wajen cike gibin bin ka’idoji da ya dade yana wanzuwa.
Rahoton ya tabbatar da cewa sakamakon kyawawan gyare-gyaren kasa baki daya da kuma karfafa sa ido da aiwatar da doka, Nijeriya ta fice daga jerin “Grey list” na Financial Action Task Force (FATF). Wannan ya zama wani muhimmin mataki wajen dawo da amincewar kasa da kasa da kuma rage matsalolin bin ka’idoji a harkokin kudi na ketare iyaka.
Ba tare da jayayya ba, kyakkyawan suna na daya daga cikin mafi muhimmancin kadarorin kowanne tsarin kudi. Saboda haka, ga Nijeriya, batun suna ba wai kawai na fahimtar jama’a ba ne, har ma da na manufofi, juriyar tsari, da haduwa da tsarin kudi na duniya.
Abin farin ciki ne ganin cewa al’ummar fintech sun fahimci kalubalen da ke akwai, kuma tuni suka fara inganta gyare-gyare da ke hada ingantacciyar aiwatar da fasaha da kuma bayyananniyar sadarwa, tun daga aiwatar da dokokin AML, kare hakkin masu amfani, har zuwa sabbin hanyoyin sa ido da kulawa.
Wadannan matakai na nuna kuduri mai karfi na sake gina amincewa, fadada shigar jama’a cikin harkokin kudi, da kuma sanya Nijeriya a matsayin kasa abin dogaro kuma mai gasa a tsarin kudi na duniya.
Binciken da (CBN) ya gudanar tare da masu ruwa da tsaki ya fi dogaro ne da ra’ayoyin kamfanonin fintech, wanda ya ba da cikakken hangen nesa kai tsaye kan dama da kalubalen da masu kirkire-kirkire ke fuskanta a sahun gaba na tsarin fintech a Nijeriya.
Babban bankin ya bayyana a sarari cewa zai kasance da amfani a fadada wannan tattaunawa ta hanyar hada sauran muhimman masu taka rawa a tsarin, domin hakan zai zurfafa fahimta game da tsarin gaba daya, tare da karfafa bukatar tsari mai cikakken hangen nesa wajen tsara manufofi da bunkasa masana’antar fintech.
Dangane da wannan tunani, kuma a cikin dimbin bayanai da aka tattara, wadannan su ne wasu daga cikin muhimman darussa da rahoton ya bayyana:
CBN yana sane da cewa bunkasar kasuwanci a ketare na bukatar hadin kai: Tuni, kashi 62.5 cikin 100 na kamfanonin fintech suka zama suna da shirin fadada ayyukansu a matakin yanki. Wannan yana samun goyon baya ne ta hanyar karfafa tsarin Takardar izinin aiki bisa ƙa’idoji a kasuwanni daban-daban, wanda zai ba da damar fadada kasuwanci cikin sauki da bin ka’idoji a kasuwannin Afirka masu kama da juna.
Rahoton ya gane cewa Fasahar Wucin Gadi (AI) da tsarin biyan kudi na kai-tsaye (real-time payments) ba za a iya gujewa tasirinsu ba wajen haifar da sabon zamani: musamman ma AI, ana amfani da ita sosai wajen ganowa da hana damfara da kuma tantance cancantar bashi (credit scoring). Haka nan, tsarin biyan kudi na kai-tsaye ana kallonsa a matsayin mai karfi da kuma misali ga sauran hanyoyin dijital na kudi.
Rahoton ya amince cewa gibin cibiyoyin more rayuwa na ci gaba da zama kalubale, inda masu ruwa da tsaki suka nuna cewa rashin samun dama ta kowa wajen tabbatar da ainihin mutum ta dijital, karancin yaduwar ‘broadband’, rashin cikakken tsarin musayar bayanai (data-sharing systems), da iyakancewar tsarin bude bayanai (open-data frameworks) suna zama manyan shingaye ga bunkasar tsarin.
Haka kuma, rahoton ya nuna cewa kimar bin ka’idoji na sanya cikas ga kirkire-kirkire: Misali, kashi 87.5 cikin 100 na wadanda aka tambaya suna ganin cewa tsadar biyan bukatun dokoki da hadarin kasuwanci yana tasiri sosai wajen iyawarsu na kirkire-kirkire.
A cikin wannan rahoto, CBN ta bayyana manyan manufar mataki uku da za su jagoranci dabarun fintech na Nijeriya. Bisa ga haka, ta fayyace muhimman fannonin fifiko don makomar fintech ta kasar, bisa ga sakamakon binciken ra’ayi da nazarin manufofi.
Wadannan sun hada da: 1 Kirkirar dokoki masu karfafa kirkire-kirkire: Saukake tsarin amincewa da sabbin abubuwa,. Kara bayyananniyar jagora daga masu tsara dokoki. Amfani da fasahar sa ido (SupTech) don rage cunkoso da matsaloli.
Karfafa shigar jama’a cikin harkokin kudi ta hanyar fasahar dijital (financial inclusion):
Kyautata inganci da tsadar samun damar amfani da API ga tsarin ainihin mutum na kasa,
Karfafa hadin kai tsakanin dandamali na dijital. Inganta juriyar cibiyoyin more rayuwa domin cike gibin da ke tsakanin tsarin da masu amfani, musamman a kauyuka da kananan unguwanni.
Karfafa sahihanci da suna, da kare masu amfani. Sabunta tsarin kare masu amfani da shi,
Karfafa sanya ido kan yaki da halatta hanyoyin samun haramtattun kudade (AML superbision),
Bayyana sakamakon gyare-gyare ga jama’a da masu ruwa da tsaki.
Rahoton ya bayyana cewa, da wadannan manufofi a gaba, kuma daidai da bayanan da (CBN) ya yi na kyakkyawan tsarin gyare-gyare, ingancin kudi, da aiwatar da manufofi bisa hujjoji, akwai bukatar aiwatar da shirye-shirye da dama na manufofi, ciki har da:
Dandalin tattaunawa na musamman tsakanin CBN da fintech. Samfurin bin ka’idoji a matsayin ayyukan yau da kuluum. Shirin bayar da garanti na bashi ga kamfanonin fintech. Fadada tsarin ‘Open banking’. Gwajin yarjejeniyoyin a matakin yanki.
Wadannan matakai suna da muhimmanci wajen tabbatar da cewa tsarin fintech na Nijeriya ya ci gaba da bunkasa cikin tsari, amintacce, kuma mai tasiri.
Rahoton CBN ya kuma bayyana cewa sakon gaggawa daga tsarin fintech shi ne cewa hadin gwiwa ba zai iya kasancewa ta hanya ta wucin gadi ba. Dole ne ya kasance ana yin sa akai-akai, kuma bisa amincewa mai karfi. Kamfanonin fintech suna shirye su yi hadin gwiwa. Masu tsara dokoki kuma suna bude sabbin hanyoyi. A ganinsu, yanzu ne lokacin da za a tabbatar da wannan karfi da kuma kafa tsarin shugabanci da zai tallafa wa alhakin juna.
Tare da gyare-gyare masu dacewa da kuma hangen nesa guda, Nijeriya za ta iya tashi daga kasancewa jagora wajen fintech zuwa mai tsara ka’idoji a fintech. Wannan rahoton an yi shi ne domin tallafawa wannan tafiya ta hanyar bayanai, fahimta, da buri na hadin gwiwa.
Uzodinma ma’aikaci a Magnificat Synergy Ltd.















Discussion about this post