Connect with us

NOMA

Kasafi: Nijeriya Ta Saba Alkawarin Maputo Kan Kebe Wa Noma Kashi 10

Published

on

Wani rahoto ya ce, duk da bukatar Maputo ta watan Yulin shekarar 2003 data bukaci a ware kashi 10 a cikin dari a don fannin noma a cikin kasafin kudi, wadda kuma Nijeriya tana daya daga cikin yarjeniyar da aka kulla, baifi kashi 5 gwamnatin tarayya take warewa fannin bay au kimanin shekaru 17 da kulla yarjejeniyar.

Hakan ya janyo koma baya ga fannin na noma a Nijeriya, inda kuma aka bar Nijeriya a baya wadda take da eka sama da miliyan 84 da za’a iya yin noman Rani, hakan ya kuma sanya Nijeriya ta koma tana bin bayan kasashen Kenya, Afirka ta Kudu, Zambia, Ethiopia da kuma Rwanda.
Har ila yau, ricikin dake yawan aukuwa a tsakanin manoma da Fulani makiyya, inda hakan yake janyo zubar da jnin alumma hjakan ya kuam kara zamowa wani tirniki ga manoman dake kasar nan.
Ma’aikatar aikin nomad a raya karkara ta tarayya ta nuna bukatar kashe sama da naira biliyan 9 don bunkasa fannin noma akan kuma amfanin gona iri-iri.
Sai dai, kalubalen kamar yadda wasu masu fashin baki a fannin suke gani, duk da kasafin da aka warewa fannin, kwalliya bata biyan kudin Sabulu.
Amma a na samun nasara ne kawai daga tallafin da ake samu daga gun kungiyoyin aikin noma na kasa da kasa.
Bugu da kari, a kan samar da hanyoyi a karkara da samar da ingantaccen ruwan sha, ma’aikatar ta na son kashe naira biliyan 7.64.
Sun kuma lura cewa, mafi yawancin hanyoyin dake a karkara, ayyukansu sun fada ne a cikin ayyukan mazabun da yan siyasar da aka zaba suka fito hatta manyan fitilun kan hanya.
Dangane da abinci da dabarun adana abinci wanda aka dinga sukar gwamnati kanbrashin samar da kyakyawan tsarin adana abincin da zai rage radadin karancin abincin da ake dashi a kasar nan, an kebe naira biliyan 2.01 din samar da rumbunan zamani na adana hatsi, sai dai, rumbunan an bayar da aikin yin su ta hanyar jingina a karkashin yarjejeniyar tsarin PPP
Sai dai, kwarru a fannin aikin noma a kasar nan sun sanar da cewa, Nijeriya tan a bukatar Taraktocin noma a yanzu guda 750,000 don biyan bukatar Manoman dake a kasar nan.
Nijeriya dai bata kera Taraktocin noma tana shigo dasu ne kawai cikin kasar nan.
Amma akwai kanan Taraktocin noma da Cibiyar yin noma da kayan noma na zamani ta kasa NCAM da ke a garin Ilorin a jihar Kwara take sarrafawa.
Har ila yau, gwamnatin bata da kuma bayar da wani rangwame ga Manoman dake a karkara don su samar da amfanin gona mai yawa a kasar nan.
Wasu daga cikin Manoman sun bayyana cewa, za’a barsu a baya wajen yin nomad a kayan aikin noma na zamani, in har gwamnatin bata bayar da taimakon da ya kamata ba, musamman don a daukaka fannin samar da kayan aikin noma na zamani a kasar nan.
Shugaban kungiyar masu noma Tumatir na kasa Alhaji Abdullahi Ringim NTGPAN ya shawarci Gwamnatin Tarayya data fito da tsarin day a kamata yadda Manoman kasar nan zasu daina yin aikin gona da tsari na al’ada da aka saba dashi a kasar nan.
Ya yi nuni da cewa, an jima a Nijeriya ana yin hada Taraktocin noma, inda kusan aka shafe shekaru da dama, inda ya yi nuni da cewa, mun tsallaka daga Fartanyu zuwa Taraktocin noma amma kasar China ita kuma ta tsallaka daga yin amfani da Fartanyu zuwa yin amfani da Taraktocin noma na hannu.
A cewarsa, Nijeriya ta na da kasar fadin noma mai giraman gaske, inda mafi yawancin Manoman kasar su ke da daga kadada daya zuwa kadada biyar.
Shugaban kungiyar masu noma Tumatir na kasa Alhaji Abdullahi Ringim NTGPAN kasashen da ke a kasar waje suna baiwa kasashen kwarin gwaiwa sayen Taraktocin noman da suka kera.
A cewar Shugaban kungiyar masu noma Tumatir na kasa Alhaji Abdullahi Ringim NTGPAN, dukkan wadannan shekarun da aka shafe, kasashen basu zo sun koyar fasaha kan yadda za’a kera Taraktocin noma ba a Nijeriya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: