Kasar Sin ta kammala aikin samar da babban bangaren tashar tura iskar carbon dioxide cikin kasa, da ke cikin teku, yayin da sabon dandalin rijiyar hakar iskar gas ta Dongfang1-1 ta shiga matakin kaddamarwa a yau Lahadi.
Wannan aiki na gwaji, an tsara ta yadda zai rika tura iskar carbon dioxide da aka tara zuwa karkashin kasa domin bunkasa samar da iskar gas. Da zarar tashar ta fara aiki, za ta ba da damar adana ton sama da miliyan 1 na carbon dioxide a kowacce shekara, lamarin da zai rage fitar da hayaki mai guba a babban mataki, a masana’antar makamashi ta Sin ta cikin teku.
Dandalin zai tara tare da tace carbon dioxide da aka samar tare da iskar gas, sannan ya matse, ya mayar da shi karkashin kasa. Wannan aiki zai inganta hakar iskar gas da kuma adana iskar carbon dioxide har abada.
Rijiyar hakar iskar gas ta Dongfang 1-1, ita ce irinta ta farko da Sin ta samar da kanta, wadda ke cikin teku, kuma babbar rijiyar hakar gas mafi yawan iskar Carbon dioxide. Tun bayan fara aiki a 2003, ta samar da iskar gas cubic mita sama da biliyan 50. (Fa’iza Mustapha)














