Wakiliyar dindindin ta kungiyoyin agaji na Red Cross da Red Crescent na kasa da kasa (IFRC) a kungiyar Tarayyar Afrika da hukumomin kasa da kasa Asha Mohammed, ta ce suna daukar ayyukan hadin gwiwa da kasar Sin a matsayin mai matukar ma’ana kuma suna sa ran kara karfafawa da fadada hadin gwiwa da kasar a karin bangarori.
Asha Mohammed wadda kuma ke jagorantar tawagogin IFRC na kasashen Habasha da Djibouti, ta bayyana haka ne yayin hirar da ta yi da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, a gefen taron kara wa juna sani kan karfafa juriyar al’umma ga kungiyoyin agaji na Red Cross da Red Crescent, karkashin tsarin hadin gwiwar Sin da Afrika da ya gudana a Beijing.
Cibiyar horo ta kungiyar Red Cross ta Sin ce ta karbi bakuncin taron na makonni 2 a watan Satumba, wanda kuma ya samu goyon bayan kungiyar IFRC
Wakilai 26 daga kungiyoyin Red Cross da Red Crescent na kasashen Afrika 19, tare da wakilan IFRC, sun halarci lakcoci tare da yin ziyarce-ziyarce da tattaunawa yayin taron, inda suka yi musayar dabaru da daukar darusa daga dabarun Sin wajen rage barazanar annoba da kara juriyar al’ummomi da samar da ci gaba mai dorewa.
A cewar Asha Mohammed, kasar Sin tana shiga ayyukan karfafa kwarewa a matakin Kungiyar Tarayyar Afrika, ciki har da wadanda ke mayar da hankali kan wadatar abinci da tsare-tsaren kiwon lafiyar al’umma, kuma tana gabatar da dabarunta masu daraja. (Fa’iza Mustapha)














